Home / Big News / Abdul’aziz Yari Zai Sake Shimfida Kafet A Masallacin Sultan Bello

Abdul’aziz Yari Zai Sake Shimfida Kafet A Masallacin Sultan Bello

 

…..Ayi koyi Da Sanata Abdul’aziz Yari
Daga Imrana Abdullahi
A kokarinsa na ci gaba da taimakawa addinin Musulunci tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Sanata Abdul’aziz Yari, Shatiman Zamfara kuma Marafan Sakkwato ya bayyana wa shugabannin masallacin Sultan Bello da ke Kaduna cewa zai sake shimfidar masallacin ta Kafet baki daya.
Sanata Abdul’aziz Yari ya dai bayyana hakan ne a cikin masallacin a yau ranar Juma’a 16 ga watan Janairu, 2026, a lokacin da ya ke cikin masallacin domin gabatar da sallar Juma’a.
.
Shugabannin masallacin ta bakin mai sanarwa a Masallacin ya tsaya a gaban jama’a a cikin masallacin kafin gabatar da sallar juma’a ya bayyana sunan Sanata Abdul’aziz Yari da cewa shi ne zai Shimfida Kafet a dukkan cikin masallacin baki daya.
Shima Limamin Juma’a na masallacin tun kafin ya gabatar da huduba sai da ya bayyana cewa wani bawan Allah zai Shimfida Kafet a wannan masallaci baki daya, amma kuma sai shi mai gabatarwa a Masallacin ya gaya wa jama’a cewa Sanata Abdul’aziz Yari ne zai Shimfida Kafet din baki daya.
India za a iya tunawa ko a shekarar da aka yi cutar Korona sai da Sanata Abdul ‘aziz Yari ya bayar da gagarumar gudunmawar taimako a wannan masallacin na Sultan Bello da ke Kaduna.
Kuma Sanata Abdul’aziz Yari ne mutumin da ke raba wa bayin Allah kayan abinci a jihar Zamfara wanda ko a shekarar da ta gabata sai da ya rabawa mutane Tirelolin abinci har sama da  guda dari da Saba’in ga al’ummar jihar Zamfara a watan Azumi duk da nufin su samu saukin rayuwa.
Kuma a bisa zance na gaskiya Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar Shatiman Zamfara kuma Marafan Sakkwato ne mutumin da idan an kiraye kirayen ya tsaya takara zaka ga abokan arziki da sauran daukacin al’umma za su tara abin da su da kansu za su yi kamfen da shi domin kawai nuna gamsuwa da irin yadda Sanata Yari ya dade ya na tawainiyar da su har suka zama wani abu a cikin duniya su rika yin kamfen har sai an samu nasarar da kowa ke bukata, kuma a Jihar Zamfara a zaɓen da ya gabata nasarar lashe zaben Sanata Abdul’aziz Yari ce aka fara bayyana wa bayan gudanar da zaben wanda Ni ina cikin manema labaran da ya tattauna da su bayan kammala yin Limancin sallar La’asar a Masallacin gidansa da ke garin Talatar Mafara cikin Jihar Zamfara a Arewacin Tarayyar Najeriya.

About andiya

Check Also

Cloves farming pilot in Nigeria is significantly gaining Momentum.

By; Imrana Abdullahi Members of the Cloves Producers, Processors, and Marketers Association in Nigeria paid …

Leave a Reply

Your email address will not be published.