Home / Labarai / Abdulrasheed Bawa Ya Nemi In Bashi Cin Hancin Dala Miliyan Biyu – Gwamna Matawalle

Abdulrasheed Bawa Ya Nemi In Bashi Cin Hancin Dala Miliyan Biyu – Gwamna Matawalle

A cikin wadansu kalamai da bangarori biyu na Gwamna Matawalle na Zamfara da kuma shugaban hukumar Efcc suka yi wa Juna ya sa muka yi maku tsakure a kan kalaman nasu kamar yadda suka gudana.

 

Gwamnan Jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya zargi shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa, da cewa ya nemi cin hancin dala miliyan Biyu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da ake cikin wata Takin saka mai tsanani tsakanin Gwamnan da kuma hukumar ta Efcc.

A cikin wata takardar sanarwa da Gwamna Matawalle ya fitar a ranar Laraba, inda ya bukaci Bawa da ya ajiye aikinsa, ya na mai cewa ya na da tambayoyin da zai amsa a game da batun Cin hanci.

Amma shi kuma shugaban na Efcc ya fito fili ya bayyana cewa babu wani abin da yake boyewa sai ya gayawa Matawalle cewa in har ya na da wadansu Zarge zargen da yake yi sai ya rubutawa hukumomin da ya dace masu gudanar da bincike idan ya na da hujja a kansa.

 

A cikin wata tattaunawar da ya yi da gidan rediyon bbc Hausa, Matawalle ya kara jadda da cewa ba ta yadda za a yi a amince da Bawa.

 

 

 

“Ba wai kawai a koda yaushe ba a rika zargin Gwamnoni ba haka kawai, domin ba wai Gwamnoni ba ne suke da shi. Shin me shugaban hukumar Efcc ya yi masu? da har yake ikirarin cewa ya na da hujja a game da abin da suka aikata wato Gwamnonin, in har haka ne ya dace ya nunawa duniya abin da yake da shi na hujja kuma su kuma wadanda suke aiki a matakin Gwamnatin tarayya kuma da.

“Idan ya bar ofishin da yake aiki, mutane za su tabbatar da cewa shi ba abin amincewa ba ne, ina shaida maku cewa a cikin dakikoki 10 mai yuwuwa sama da mutane 200 za su kawo hujjojin cin hanci da rashawa da ya karba daga hannunsu. Ya kuma san abin da ya nema daga gare ni amma na ki amincewa.

“Ya nemi in bashi Cin hanci na dala miliyan Biyu kuma duk ina da hujja a kan abin da nake fadi. Ya kuma san gidan da muka hadu, ya fayyace ni ya kuma gaya Mani yadda ake yi ko za a yi. Ya ce Mani Gwamnoni na zuwa ofishinsa amma ni Bana zuwa.Idan ba ni da hujja, ba zan fadi wannan maganar da nake fadi ba”.

Da aka tuntube shi domin jin ta bakinsa, kakakin hukumar Efcc Wilson Uwujaren,cewa ya yi bai ha labarin ba don haka ba zai yi magana a kai ba.

Da aka gaya masa cewa a gidan rediyon bbc hausa ne Gwamna Matawalle ya yi maganar, sai ya ce shi baya jin hausa sai ya ce a aika masa da labarin domin ya mayar da martani a kan batun, amma dai har ya zuwa lokacin hada rahoton ba a ji komai ba daga gare shi ba . ( kamar yadda jaridar daily trust na ruwaito).

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.