Home / Kasuwanci / ABOKAN CINIKI DA DILLALAI SUN YABA WA DANGOTE SABODA KARFAFA SU DA KUMA GOYON BAYA DA YAKE BA SU
DSC, 7735, 7734, & 7689, L--R, Best overall winner, Otunba Kazeem Olayemi Odeyeyiwa, FCA, of the Kazab Heritage, Dangote Cement plc Group Managing Director ,Arvind Pathak, Wife of the Best Overall Winner, Yeye Adesola Mutiat Odeyeyiwa, Chairman of Dangote Cement plc, Aliko Dangote, second Best winner, Chief Gilbert Igweka, and his Wife Perpetua, of Gilbert Igweka Global Concept, Third Best Winner, NWA Ado, of Nwa Ado Resources Nig.Enterp. at the Dangote Cement plc, Distributors Awards Nite, in Lagos on Friday 26th January 2024

ABOKAN CINIKI DA DILLALAI SUN YABA WA DANGOTE SABODA KARFAFA SU DA KUMA GOYON BAYA DA YAKE BA SU

 

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna

 

 

Abokan ciniki da dillalan kamfanin siminti na Dangote sun yaba wa shugaban kamfanin kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote.

Sun bayyana cewa tausayi da karamcin Dangote ne suka sanya ya tsere wa tsara a harkokin kasuwanci a Najeriya da kuma nahiyar Afirka baki daya..

Da suke bayanin a yayin bikin karrama abokan hulda da kamfanin simintin Dangote na shekarar 2023 da aka gudanar a karshen mako a Legas, abokan huldan wadanda suka fito daga ko’ina a fadin kasar nan, sun bayyana dangantakar kasuwancinsu da kamfanin Dangote a matsayin ‘kyakkyawar alaka’ da mai kaunar ganin abokin hulda ya cigaba.

A lokacin bikin dai an raba wa dillalai kyaututtuka masu gwabi saboda imanin da suka yi da kamfanin siminti na Dangote ta hanyar cigaba da sayen kayayyakinsa.

Baya ga mawaka irin su Kizz Daniel da Tuface Idibia da suka cashe baki a lokacin bikin, akwai kuma wadansu fitattatun manyan Najeriya da suka halarci bikin domin taya Dangote da abokan huldar Kamfanin murna.

Daga cikin manyan bakin da suka halarta akwai, tdohon gwamnan jihar Ekiti, Dokta Kayode Fayemi da shugaban
kamfanin Geregu Power, Femi Otedola da kuma tsohon ministan Masana’antu da Ciniki da harkar Zuba jari, Otunba Niyi Adebayo da kuma sauran manyan baki da dama. Kamfanin Kazab Heritage ne ya samu kyautar dillali na shekara, a yayin da kamfanin Gilbert Igweka Global Concept, ya zo na biyu, kamfanin Nwa Ado Resources Nigeria ya zo na uku.

Wadanda suka samu nasara daga yankunan kasar nan kuwa sun hada da : Kamfanin Twins Faja Enterprises, wanda ya zo na daya a yankin Legas/Ogun, sai Nwa Ado Resources Nigeria, da ya zo na daya a yankin Arewa ta tsakiya, sai kuma Abdullahi Fugu, da ya zo na daya a yankin Arewa Maso Gabas, akwai kuma Giwa Dynamis Ventures, da ya zo na daya a yankin Arewa Maso Yamma da kuma D.C.Okika Nigeria Limited, wanda ya zo na daya a yankin Kudu Maso Gabas.

A cewar shugaban kamfanin Twins Faja Nigeria Limited, Mista Wale Fajana, ‘ na kwashe fiye da shekara 20 ina dillancin simintin kamfanin Dangote, kuma tun daga lokacin harkar kasuwancina take habaka kamar wutar daji.”

Ya bayyana cewa, ya fara harka da kamfanin Dangote ne tun kamfanin yana Apapa, kuma tun daga lokacin ‘ Alhaji, ya ce, shi da abokan cinikinsa sun yi matukar amfana da kamfanin siminti na Dangote a cikin shekaru masu yawa da suke hulda da shi.

Shi kuwa Alhaji Abdullahi Fugu, na A.A.Fugu &Sons, wanda yake zaune a yankin Arewa Maso Gabas na Najeriya, cewa ya yi, ya fara hulda da kamfanin siminti na Dangote ne da karamin jari, amma saboda taimako da goyon bayan da ya samu a wurin Dangote, da kuma jami’an gudanarwar kamfanin, yanzu ya zama babban dillali na kayan kamfanin. Ya kara da cewa, “Alhaji Dangote mai karamci ne sosai, “shawarwarinsa sun taimaka wajen bunkasa kasuwancina. Kuma kamfanin ya taimaka wa dillalansa sun daukaka harkarsu, kuma ya dauki mutane aiki. a cewar Fugu.

A nasa bangaren, shugaban kamfanin Nwa Ado Multi Biz, Cif Akukalia Igwebuike, wanda yana cikin manyan diloli guda uku, ya alakanta nasarar da ya samu ne a kan goyon bayan da ya samu daga kamfanin Dangote, musamman Aliko Dangote, wanda ya ce ya yi kokari kwarai wajen ganin kasuwancinsa ya bunkasa, kuma a kowane lokaci yana ba shi shawara domin cigaban harkar kasuwancinsa. “Babu abin da zan ce sai godiya ga Alhaji, saboda taimakawar da ya yi wa harkar kasuwancina. Don haka na yi alkawarin kara jajircewa a wannan shekara ta 2024 domin in tashi daga matsayin na uku zuwa matsayi na gaba a cikin dillalan kamfanin.”

A nata jawabin, Misis Beatricr Chinwe Okika, shugabar D.C.Okika Nigeria Ltd, wacce babbar dila ce a yankin Kudu Maso Gabas, cewa ta yi, alakarta da Dangote ta wuce ta kasuwanci, ‘ domin tun daga lokacin da mijina ya rasu Dangote yake taimaka mun tare da kasuwancina.”

“A kowane lokaci yana kulawa da iyalina da kasuwancina, yana kuma taimakawa da kudi da bayar da taimako iri-iri domin taimaka wa iyali da kasuwancina, taimakon da Dangote yake mini ba ya kidayuwa.”

A cewarta, kamfanin siminti na Dangote yana cigaba da taimaka wa duk dillalansa domin kara dankon alakarsu. Allah Ya akbarkace shi, Ya kuma cigaba da yi masa jagora.”

Shi ma Injiniya Festus Abononkhua, na kamfanin Raybale Nigeria Ltd, bayyana Dangote ya yi da cewa abokin huldar kasuwanci ne mai nagarta.

Ya ce, da farko a matsayinsa na Injiniya har kunya yake ji a ga yana dillancin siminti, amma yanzu yana matukar alfahari da kasancewa dilalin simintin Dangote.

Ya kara da cewa, a yau da taimakon kamfanin simintin Dangote harkar kasuwancinsa ta bunkasa sosai a yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya.

About andiya

Check Also

RE: ALLEGATION OF EXTORTION BY OFFICER OF THE NGERIA CUSTOMS SERVICE FEDERAL OPERATIONS UNIT ZONE ‘B’ AT MOKWA AXIS OF NIGER STATE

      (1) The Comptroller Federal Operations Unit Zone ‘B’ Kaduna, Comptroller Dalha Wada …

Leave a Reply

Your email address will not be published.