Home / Labarai / Aikin Mu Shi Ne Mu Tabbatar An Yi Aiki Da Doka – El- Rufa’i

Aikin Mu Shi Ne Mu Tabbatar An Yi Aiki Da Doka – El- Rufa’i

Aikin Mu Shi Ne Mu Tabbatar An Yi Aiki Da Doka – El- Rufa’I
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i, ya bayyana cewa aikinsu a matsayin Gwamnati shi ne su yi aikin ganin an yi aiki da doka kamar yadda tanaje tanajen dokar ya tanadar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin taron masu ruwa da tsaki a kan harkokin tsaro.
Shi dai wannan taro dai an yi shi ne a dakin taro na gidan Gwamnatin Jihar Kaduna fadar Gwamnatin Jihar.
El-Rufa’i ya bayyana cewa hakika ba aikin Gwamnati ba ne ko su da suke aikin tafiyar da Gwamnati su ce sai sun tattauna da yan bindiga ko masu satar mutane da sauran wadanda suke daukar doka a hannunsu su na aiwatar da ta’addanci iri iri a cikin kasa, wanda sanadiyyar hakan yake haifar da asarar dimbin Dukiya da rayukan jama’a.
Taron masu ruwa da tsakin dai da suka halarci taron sun hada da shugabannin kungiyoyi, Sarakunan Gargajiya, shugabannin addini sakamakon fadada yawan mahalarta taron domin samun cimma nasarar da ake bukata.

About andiya

Check Also

Muna Kokarin Kafa Hukumar Da Za Ta Hada Hukumomi Wuri Daya Ne – Honarabul Gumi

Bashir Bello majalisa Abuja Honarabul Suleiman Abubakar Gumi wakilin kananan hukumomin Gumi da Bukkum a …

Leave a Reply

Your email address will not be published.