Home / Kasuwanci / Aikin Tsaftace Gari Gwamnatin Kaduna Ke Yi – Aliyu Tanimu Zariya

Aikin Tsaftace Gari Gwamnatin Kaduna Ke Yi – Aliyu Tanimu Zariya

Aikin Tsaftace Gari Gwamnatin Kaduna Ke Yi – Aliyu Tanimu Zariya

Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban kungiyar Direbobin Mota ta kasa (NURTW) reshen Jihar kaduna Alhaji Aliyu Tanimu Zariya ya bayyana abin da Gwamnatin Jihar Kaduna take yi na hana tashoshin kan hanya a matsayin tsaftace garuruwa da Jihar baki daya.
Alhaji Aliyu Tanimu ya bayyana cewa kamar yadda kowa ya Sani akwai tsari da ka’idar yin amfani da tashoshin motar daukar jama’a kamar yadda lamarin yake a tsare don haka wadanda suka je wadansu wurare suka yi kaka gida a bakin tituna da sunan tashoshin mota ba su da hurumin yin haka a bisa doka da ka’ida.
Aliyi Tanimu Zariya ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Ofishinsa da ke Kaduna.
Ya ce ” wadansu mutane da suka mayar da tashar motar da aka yi domin daukar fasinjoji amma suka mayar da wuraren ajiyar Tankuna, kayan Gwangwanaye da sauran kayayyaki da ba wadanda aka tanaji wurin domin su ba hakika sun sabawa doka kuma ba su da wani hurumin yin hakan”.
Shugaban ya bayyana wadanda ke yin banga bangar daukar fasinjoji matafiya a gefen tituna da cewa mutane ne da ba su da tabbas ta fuskar tsayar da farashin hawan mota da kuma tsare dukkan wata ka’idar da aka tanadar domin yin sana’ar sufurin daukar fasinja daga wannan wuri zuwa wancan.
Ya ci gaba da bayanin cewa a kan kokarin tsare ka’ida ne yasa su a matsayin babbar kungiyar ta kasa suke a wuri daya a ko’ina cikin tashoshin mota suna daukar fasinja a kan farashi daya tare da tsare duk wata ka’idar da aka tanada a kasa domin habbaka tattalin arzikin kasa baki daya.
Sai ya yi kira ga daukacin yayan kungiyar NURTW ta kasa da su ci gaba da aiki tare da bin doka da ka’idar da aka tanadar kamar yadda aka san kungiyar a fadin kasa baki daya.
Ya kara fadakar da direbobi da su kula da wannan lokacin da ake ciki na watannin karshen shekara da ake kira watannin emba da ake samun karin yawaitar matafiya a ciki da wajen kasar baki daya
Ya kara jaddada cewa kungiyar za ta ci gaba da yin tarurrukan fadakar da direbobi kan muhimmancin kiyaye doka da kuma tuki cikin natsuwa domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
” Mu a cikin tashoshin mota da muke daukar fasinja ba mu da wani direba mai san kowace irin kwaya domin gudanar da aiki musamman a wannan lokaci na watannin karshen shekara, don haka nake gayawa jama’a da babbar murya kan idan za su yi zargi su daina Dora tunanimsu a kan masu daukar fasinja a cikin tashoshin mota wadanda aka tanada domin yin hakan, saboda wadansu ne daga wajen tashar mota masu banga bangar daukar jama’a a gefen tituna keda wannan akida ta sai an yi sauri”.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga Gwamnati domin ta samu sukunin sauke nauyin da ke kanta tsaftace wurin da aka kebe domin daukar fasinja.

About andiya

Check Also

Union Across River Niger: New Nigerian Editor Brother’s Wedding Grounds Makurdi

    Makurdi the capital of Benue State was agog all through the weekend, as …

Leave a Reply

Your email address will not be published.