Home / Uncategorized / AIWATAR DA KASAFIN KUƊI: KU DAINA YAƊA RAHOTON ƘARYA, GWAMNATIN ZAMFARA GA SAHARA REPORTERS

AIWATAR DA KASAFIN KUƊI: KU DAINA YAƊA RAHOTON ƘARYA, GWAMNATIN ZAMFARA GA SAHARA REPORTERS

 

Gwamnatin jihar Zamfara ta taka wa Sahara Reporters burki dangane da labaran ƙarya da kafar yaɗa labaran ta intanet ke yaɗawa game da yadda aka tafiyar da kuɗaɗen tsaro na jihar.

Jaridar Sahara Reporters ta buga wani labari a ranar Juma’a mai taken ‘Duk Da Rashin Tsaro, Gwamnatin Zamfara Ta Kashe Naira Miliyan 30 Kan Tsaron Cikin Gida, Inda Ta kashe Naira Biliyan 3.6 A Harkokin Tafiye-tafiyen Ƙasa Da Ƙasa A 2024’.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana rahoton da Sahara Reporters ta wallafa a matsayin wani labari na batanci da ake ta yaɗawa domin yaudarar al’umma.

Sanarwar ta ƙara da cewa, labarin ya bayyana gazawar Sahara Reporters ta hanyoyi biyu: rashin himma wajen duba takardar kasafin kuɗi ko irin salon aikin jaridar su ta ‘ba ni na iya’

“An ja hankalinmu kan wani labari na ƙarya da wani dandali yaɗa labarai na yanar gizo, Sahara Reporters ya ruwaito, yana mai cewa gwamnatin jihar Zamfara ta kashe Naira miliyan 30 wajen tsaron cikin gida a shekarar 2024.

“Labarin ba wai kawai ƙarya ba ne, amma wani salo ne da nufin yaudarar jama’a.

“Mun zamanantar da tsarin kasafin kuɗinmu, inda muka saka komai a gidan yanar gizon gwamnatin jihar Zamfara – www.zamfara.gov.ng, don haka jama’a za su iya karantawa tare da samun sahihin bayanai a maimakon bayanan ƙarya da kafar yanar gizon ta zaba.

“Kuɗaɗen da ake kashewa kan harkar tsaro ya ƙunshi abubuwa da dama. Muna da Ma’aikatar Tsaro ta Cikin Gida da Ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha, wanda ke gudanar da al’amuran tsaro.

“Ma’aikatar Tsaro ta Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida tana da lamba ta 01240000000 na tattalin arziki a takardar kasafin kuɗi.

“Shafi na 31 na wannan takarda ya nuna cewa ma’aikatar tsaron cikin gida ta kashe N1,011,695,854.50, inda ta samu kashi 104 a shekarar 2024.

“Rashin himma da doɗewar basira ta Sahara Reporters ya hana ta ganin shafi na 41 a ƙarƙashin sauran ayyuka na da dama. Mun kashe 1,267,716,000.00 akan ayyukan tsaro, wanda kashi 80 ke aiki.

“A wannan shafi na 41, an kashe wa ayyukan tsaro jimillar Naira 12,519,494,459.00, wanda kashi 72 cikin 100 na aiki.

“A shekarar 2024, gwamnatin jihar Zamfara ta kashe naira miliyan 500 domin sayen kayayyakin tsaro domin gudanar da ayyuka da dama. Wannan bayanin na ƙunshe ne a cikin wannan takarda da Sahara Reporters ta yaɗa, amma ta yi watsi da shi.

“Bugu da ƙari, jimillar kuɗaɗen da aka kashe a ma’aikatar tsaron cikin gida ya kai N207,947,374.

“Babban abin damuwa ne kuma abin dariya lura da yadda Sahara Reporters ta zabi ta raina kanta ta hanyar yin la’akari da Naira Miliyan 30 da aka ware domin tantancewa a matsayin jimillar kuɗaɗen da ma’aikatar tsaron cikin gida ta kashe. Wannan abin kunya ne da cin fuska ga aikin jarida – aikin mai daraja wanda yake mutunta labaran gaskiya.

“Godiya ga ci gaban fasaha, intanet yana bada damar tantance bayanai tare da warware shubuha. Tabbas wannan ya rage kasuwar aikin jaridar ‘ba ni na iya’ ta Sahara Reporters.

“Dalilin da ya sa muke mayar da martani ga irin wannan aikin jarida shi ne don daidaita al’amura tare da kare jama’a daga labaran ƙarya daga wata kafar yaɗa labarai da ke ikirarin tsayawa da gaskiya.

“A shekarar 2024, gwamnatin jihar Zamfara ta kashe Naira Miliyan 14,352,373,550.10 domin samar da tsaro, kamar yadda aka yi bayani dalla-dalla a cikin takardar kasafin kuɗin da ke shafinmu.

About andiya

Check Also

GOC task parents on proper upbringing of children, community service

  Maj. Gen. Ibikunle Ajose, the General Officer Commanding (GOC) 8 Division of Nigerian Army …

Leave a Reply

Your email address will not be published.