Home / Labarai / Alkalin Alkalan Jihar Kaduna Shehu Ibrahim Ya Rasu

Alkalin Alkalan Jihar Kaduna Shehu Ibrahim Ya Rasu

Mustapha Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga birnin Zariya cikin Jihar Kadina na bayanin cewa Allah ya yi wa Alkalin Alkalan Jihar Alkali Shehu Ibrahim Ahmad rasuwa.
Kamar yadda wata sanarwa da bayyana da ta fito daga Mansir Paki, sanarwar ta ce Alkalin alkalan na Jihar Kaduna ya rasu ne a ranar Litinin bayan fama da yar gajeruwar rashin lafiya.
Ya rasu ya na da shekaru 63 ya kuma bar mata hudu da yaya 19 da yan uwa da dama daga cikinsu akwai tsohon Alkalin Alkalan Jihar Kaduna Dokta Maccido Ibrahim.
An kuma shirya gabatar da Jana’iza a gidansa mai lamba 7 da ke kan titin Danburan unguwar turawa Malali cikin garin Kaduna da karfe 10 na safiya.
Allah ya gafarta masa ya kuma albarkaci abin da ya bari.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.