Home / Big News / Al’ummar Shinkafi Sun Ce Suleiman Shu’aibu Ne Sabon Dan majalisar Su

Al’ummar Shinkafi Sun Ce Suleiman Shu’aibu Ne Sabon Dan majalisar Su

 

Daga Imrana Abdullahi
Bayanan da ke fitowa daga al’ummar Karamar hukumar Shinkafi da ke cikin Jihar Zamfara na cewa daukacin wadannan al’ummar baki daya duk sun dakatar da duk wani dan takara da ke neman kujerar majalisar dokoki ta jiha da kowa ya hakura ya bar wa Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi domin samun damar ci gaba da kawo abubuwan alkairai da za su ciyar da kowa gaba.
Al’ummar Karamar hukumar ta Shinkafi, sun nuna kauna da Soyayya da kuma cewa ana tare kuma ba za su mance da irin namijin kokarin da Dokta Suleiman ke yi wa yankin ba karamar hukumar Shinkafi da kewaye ba.
” Babban dalilin da yasa muke nuna goyon bayan mu da tsananin kauna ga Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi shi ne mutum ne mai kokarin kwatowa jama’a hakkinsu a koda yaushe a fannoni daban daban saboda haka muna kyautata tsammanin cewa ko a nan gaba ma idan ya samu kujerar majalisar dokoki ta Jihar Zamfara jama’ar karamar hukumar Shinkafi za su amfana kwarai kamar yadda ya saba kokarin taimakawa tun can baya”.
” Muna kira da babbar murya ga jama’ar karamar hukumar Shinkafi da kowa ya kwantar da hankalinsa kowa ya natsu hankali ya dawo jikinsa a bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga dan takara kuma dan majalisa idan Allah ya amince da zarar aka yi zaben 2027 mai zuwa mu sai Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, muka sani a matsayin dan majalisar dokoki na Jiha da zai wakilci mutanen karamar hukumar Shinkafi baki daya, a saboda haka ne muke shaidawa xaukacin sauran yan takara da cewa su yi hakuri kowa ya bar wa Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, domin a samu ci gaban da ya dace a Shinkafi da kewaye”.

About andiya

Check Also

Gwamna Lawal Ya Jinjina Wa Dakarun Soji Bisa Nasarorin Da Suka Samu Kan ’Yan Bindiga A Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yaba wa dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Joint Task …

Leave a Reply

Your email address will not be published.