Home / Labarai / Ambaliyar Ruwa Ta Rusa Gidaje, Magidanta Na Gararamba A Kan Tituna

Ambaliyar Ruwa Ta Rusa Gidaje, Magidanta Na Gararamba A Kan Tituna

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Sakamakon mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka samu a Damaturu babban birnin jihar Yobe cikin ‘yan kwanakin nan ya haifar da gidaje da dama sun rushe  wadda hakan ya haifar da samun magidanta da iftila’in ya shafa yin Gararamba akan tituna na neman wurin da za su da fake su da iyalen su.

Wakilinmu da ya zagaya garin ya ruwaito cewa an ga wasu daga cikin wadanda bala’in ambaliyar ruwa ya rutsa da su a makale suna neman inda za su ajiye kayansu da sauran matakan gaggawa.

Rahoton ya nuna cewa matsalar ambaliyar ruwa ta zama ruwan dare a duk shekara a wasu Unguwannin garin da suka hada da  Pompomari, Sumsumma, Waziri Ibrahim, tsamiyar lilo, Nayinawa, Maisandari da Maduri saboda rashin magudanun ruwa.

A cewar rahoton, ambaliyar ruwan tana shafar dubban jama’a a cikin al’umma, yana mai jaddada cewa babu shekara guda da irin wannan al’ummar ba sa fuskantar irin wannan matsalar.

Da yake zantawa da wakilinmu daya daga cikin mazauna yankin, Malam Ibrahim kare-kare, ya ce sun sha yin kira ga gwamnati da sauran hukumomin jin kai da su kawo musu dauki, amma duk da haka babu wani martani daga bangarorin biyu.

A cewarsa, mutane da dama daga cikin al’ummar yankunan  ne suka wannan ambaliya ta tilastawa barin gidajensu sakamakon ambaliyar, inda ya ce da yawa daga cikinsu na matukar bukatar matsuguni, abinci da sauran kayayyakin agaji.

A cewar malamin al’ummomin yankunan  Maisandari, Sumsumma da tsamiyar lilo da Nainawa har yanzu suna fuskantar irin wannan kalubale, inda suka yi kira ga gwamnatin jihar Yobe da ta shigo cikin ta ta hanyar gina magudanar ruwa, titina da sauran ababen more rayuwa.

Malam Ibrahim Kare-kare sai dai kuma ya yaba da kokarin Hukumar bada  Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) kan yadda take daukar matakan gaggawa a kodayaushe, ya kuma yi kira ga wannan hukumar da ta dauki nauyin kai dauki ga wadanda wannan  ambaliyar ta shafa ba tare da wani bata lokaci ba.

About andiya

Check Also

PRESIDENT TINUBU COMMENDS DANGOTE GROUP OVER NEW GANTRY PRICE OF DIESEL

  President Bola Tinubu commends the enterprising feat of Dangote Oil and Gas Limited in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.