Home / News / PDP Shiyyar Kudu Maso Yamma Na Goyon Bayan Ayu

PDP Shiyyar Kudu Maso Yamma Na Goyon Bayan Ayu

Masu ruwa da tsaki na yan siyasa daga bangaren shiyyar Kudu maso Yamma a ranar Talata sun bayyana cikakken hadin kai da goyon baya ga shugaban jam’iyyar PDP na kasa Farfesa Iyorchia Ayu.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban masu ruwa da tsaki na PDP a shiyyar Kudu maso Yammma.
Sun jinjinawa shugaban PDP Ayu a bisa kokarinsa na tabbatar da kasa daya al’umma daya, tabbatar da Dimokuradiyya da kare dokokin Najeriya.
Fitattun shugabannin PDP, da suka yi taro a Akure, sun jinjinawa Ayu bisa kokarin da ya yi na yi wa jam’iyyar ingantaccen jagoranci.
Sun kuma yi masa jinjina da irin yadda ya dawo da martabar jam’iyyar, kara karfafa tsarin Dimokuradiyya abin da yasa jama’a suke rungumar jam’iyyar PDP a duk fadin kasa baki daya.
” A halin yanzu PDP na jin dadin irin cikakken hadin kai da aikin tare da juna”, inji su.
A matsayinsu na shugabannin yankin Kudu maso Yamma, a taron da suka gudanar hakika shugaban PDP Ayu, ya cancanci Yabo bisa kokarinsa na ciyar da jam’iyyar gaba, don haka batun da wasu mutane suke yi a kan shugaban ba abin saurare ba ne.
A cikin wata takardar da suka fitar bayan gudanar da taron mai taken, “Yankin Kudu maso Yamma sun yi magana”, shugabannin sun jinjinawa Ayu da ya kawo wadansu abubuwa da dama da ake saran za su taimaka wajen samun nasarar zaben 2023 mai zuwa.
 Takardar da suka fitar na dauke da sa hannun shugaban masu ruwa da tsaki yankin Kudu maso Yamma domon hadin kai (SWUF), Cif Ajani Bankole.
Takardar ta kara karfafa wa tare da yin Yabo na musamman ga Ayu, bisa kokarinsa na musamman domin ciyar da jam’iyyar gaba ta hanyar yin sasanci da kuma kara karfafa Gwiwa, nuna Soyayya da tsare tsaren aiki a gabanin zaben shekarar 2023.
Shugabannin sun jinjinawa Ayu game da gudunmawar da ya bayar wajen samun nasarar PDP a Jihar Osun.

About andiya

Check Also

Edo 2024: Group Hold Symposium In Support Of Asue Ighodalo

  The Good Governance Advocacy Group, has held a symposium to drum their support for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.