Home / Labarai / AN BUDE MASALLATAN DA SULEIMAN SHINKAFI YA GINA

AN BUDE MASALLATAN DA SULEIMAN SHINKAFI YA GINA

IMRANA ABDULLAHI Daga Shinkafi
A kokarin ganin an kyautatawa dimbin al’umma dangane da yin Ibadar Allah jama’a su samu sukunin yin Inada cikin natsuwa da kwanciyar hankali yasa Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya dauki aniyar Gina Masallatai a cikin garin Shinkafi da karamar hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara.
A yau ranar Juma’a ne aka yi babban taron bude masallatai guda biyu wanda Sarkin Shanun Shinkafi na farko Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya Gina domin Allah sadakatujjariya, masallatan sun hada da masallaci na yin Salloli biyar a kowace rana a Unguwar Bakin Marina Yar’aduwa tsohuwa da kuma Unguwar Kwanya Wuri duk a cikin garin Shinkafi da nufin jama’a su samu sukunin yin Sallah cikin kwanciyar hankali da lumana.
Kamar yadda Alhaji Sani Dan bara Shanawa, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Shinkafi ya bayyana a wajen taron bude Masallatan ya ce wanda aka bude a Unguwar Bakin Marina ya kai shekaru Tamanin da Biyar (85) ya na da ginin kasa, amma a yanzu an mayar da shi ginin Bulo da bulo an kuma Sanya mashi shimfidar zamani.
Sai kuma wanda aka gina a unguwar Kwanya Wuri, ya kai shekaru kusan Sittin duk ya na a matsayin ginin kasa.

About andiya

Check Also

Aliyu Sokoto tasks cabinet on transformation drive, ‘ be committed and sincere 

  By Suleiman Adamu, Sokoto SOKOTO state Governor Dr Ahmed Aliyu Sokoto has tasked members …

Leave a Reply

Your email address will not be published.