Home / Labarai / An Ci Gidan Rediyon Info 99.3 Tarar Naira Miliyan 5

An Ci Gidan Rediyon Info 99.3 Tarar Naira Miliyan 5

 Imrana Abdullahi

Sakamakon yin halin ko ‘in kula da gidan rediyon Nigeria Info 99.3 da ke yada shirye shiryensa a mita mai cin gajeren zango ya yi yasa hukumar kula da ayyukan kafofin yada labarai na rediyo da Talbijin ta kasa NBC ta yanke hukuncin cin tarar gidan rediyon naira miliyan biyar domin su gyara halinsu.

Kamar yadda hukumar NBC ta fitar da wata sanarwa cewa gidan rediyon Info 99.3  ya yi wata tattaunawa ne da wani babban mutum dan asalin tarayyar Nijeriya da ya furta wadansu kalaman da ba su da wani tabbaci kuma za su iya kawo matsala a zamantakewar yan kasa, wanda hakan ya sabawa tanaje tanajen dokokin bayar da lasisin gidan rediyo.

An dai yi hira da tsohon mataimakin Gwamnan babban Bankin Nijeriya ne mai suna Obadiah Mailafiya a cikin wani shiri mai suna “Morning Cross Fire”, da aka yayata wa duniya a ranar  10 ga watan Ogusta, 2020, daga karfe 8.30 na safe zuwa 9.00 na wannan safiyar, kamar yadda sanarwar NBC mai dauke da sa hannun hukumar ta bayyana cewa Obadiah Mailafiya ya yi kalaman da babu wata hujja kuma za su iya haifar da matsalar tashin hankali da rikici a tsakanin al’ummar kasa.

Saboda haka hukumar ta NBC ta gargadi gidan rediyon da ya guji aikata wani abu mai kama da hakan da karya dokar kasa da tanajin da hukumar ta yi wa kafafen yada labarai, in kuma ba haka ba ya fuskanci hukuncin da ya zarce wanda aka yi masa a yanzu.

About andiya

Check Also

Who Participates In The Global Economy As A Consumer. 

While noting that consumers play a vital role in the value chain as the final …

Leave a Reply

Your email address will not be published.