Home / KUNGIYOYI / Kungiyar Gwamnonin Arewa Sun Yi Kira A Bincika Zargin Da Obadiah Mailafiya Ya Yi

Kungiyar Gwamnonin Arewa Sun Yi Kira A Bincika Zargin Da Obadiah Mailafiya Ya Yi

 Imrana Abdullahi
Kungiyar Gwamnaonin arewacin tarayyar N8jeriya sun yi kira da a tabbatar da gudanar da bincike a game da irin zargin da Dokta Obadiah Mailafiya ya yi cewa wani daga cikin mambobinsu na cikin kwamandosjin kungiyar Boko Haram.
Kungiyar acikin wata takardar da ta fitar mai dauke da sa hannun Dokta Makut Simon Macham, Daraktan yada labarai da al’amuran da suka shafi wayar da kan jama’a na Gwamnan a matsayin shugaban kungiyar Gwamnonin na Arewa.
Gwamnonin sun yi kira ga jami’an tsaro da hukumominsu baki daya cewa suna kira da lallai a gudanar da ingantaccen cikakken bincike game da batun da Obadiah Mailafiya ya furta domin magana ce mai nauyi kwarai da gaske.
Cewa wani daga cikin mambobinta kwamandan Boko Haram ne a N8jeriya.”.
A cikin wata takardar da aka aikewa manema labarai a Kaduna cewa shugaban kungiyar Gwamnonin na Arewa Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya ce kungiyar ta samu kwarai a game da batun da Dokta Obadiah Mailafiya yai domin batun mai nauyi ne kwarai, don haka dole ne a gudanar da bincike a kansa.
Ya ce kungiyar tana aiki tare da Gwamnatin tarayya, hukumomin tsaro, al’umma, kungiyoyi masu zaman kansu, shugabannin gargajiya da shugabannin addini da kuma kwararru a kan harkokin ci gaba domin ganin an samu nasara a kan kungiyar Boko Haram, Ta’addanci, yan bindiga da dukkan harkokin da ke jagoranci a kan samun matsalar tsaro a dukkan yankin baki daya, don haka kalamin da Dokta Obadiah Mailafiya ya I ya cancanci a gudanar da bincike, saboda batu ne mai nauyi kwarai.
Lalong ya ce  “mu a matsayin mu na Gwamnonin arewa mun hadu a lokuta da dama mun tattauna batun matsalar tsaro a yankin arewa da kasa baki daya inda ba wai mun yi Allah wadai da lamarin kungiyar Boko Haram ne kawai ba, yan bindiga, masu fashi da makami, masu satar mutane da sauran aikata miyagun ayyuka, har ma mun samu shugaban kasa tare da sauran shugabannin tsaro duk a kokarin lalubo mafita game da matsalar baki daya.
Don haka ace wai wani daga cikin mu shi ne ke jagorantar Boko Haram a Nijeriya hakika zargi ne mai matukar nauyi da ba za a bari ya ta fi haka kawai ba. Saboda haka muke yin kiran a hanzarta gudanar da kyakkyawan bincike game da lamarin”.
Ya kuma shawarci Dokta Mailafiya da dukkan dan kasa da ke da wadansu muhimman bayanai a kan harkokin yan ta adda da ya taimakawa jami’an tsaro da kuma Gwamnati a dukkan matakai da irin bayanan sirrin da yake da su domin a dauki matakin da ya dace.
Gwamnan ya ci gaba da cewa suna dai tsammanin cewa malamai irin wadannan ba za su zamo farfagandar siyasa ba ko kuma wani yunkurin karkara da Gwamnonin na Arewa Arewa suke matukar kokarin ganin an magance matsalar tsaron baki daya a yankin.
 Simon ya kuma lashi takobin cewa kungiyar Gwamnonin Arewa ba za ta taba goyon bayan wani aikin yan ta adda ko wani ko wasu batagari ba domin a matsayinsu na Gwamnoni da iyalansu ba su tsira ba da wannan ayyukan na yan Ta’adda musamman domin ganin irin abin da ya faru ga Gwamnan Jihar Borno Babagana Zullum inda aka kai masa hari.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.