Home / Uncategorized / An Dade Da Zubar Da Shimfidar Da Sarudauna Ya Yi – Maradin Daura

An Dade Da Zubar Da Shimfidar Da Sarudauna Ya Yi – Maradin Daura

.A Kawo Karshen Matsalar Tsaron Arewa
Daga Imrana Abdullahi
Sarkin Daura Alhaji Umar Faruk, ya yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi dukkan mai yuwuwa domin kawo karshen sace- sacen jama’a da matsalar tsaron da ake yi a yankin arewa da kasar baki daya.
Sarkin ya bayyana hakan ne a wajen babban taron shekara shekara da ake yi domin tunawa da marigayi Sardauna Sa Ahmadu Bello da kungiyar tunawa da ayyukan ci gaban kasa da Sardauna Ahmadu Bello ta shirya da aka yi wa lakabi da Gamji Heritage.
A wajen babban taron an tattauna muhimman abubuwa da dama na ci gaban da marigayi Sa Ahmadu Bello Sardauna ya kawo wa kasa baki daya da a yanzu ake yin takama da su.
Sarkin na Daura ya samu wakilcin Maradin Daura Alhaji Ibrahim Muhammad Daura da ya wakilci Sarkin ya ce Sarkin Daura ya na rokon shugaban kasa da ya duba bangaren zaman lafiya a Arewa.
Ya kara da cewa idan aka yi duba sosai za a ga cewa irin shimfidar da su marigayi Sardaunan Sakkwato suka yi tuni an dade da zubar da ita saboda haka Maradin Daura ya ce lokaci fa ya yi da zamu hada hannu baki daya a ciyar da yankin Arewa gaba.
Sai Maradin Daura ya kuma yi kira ga shugabannin arewacin Najeriya da su rika yin ko yi da irin ayyukan ciyar da yankin gaba da marigayi Sardauna ya yi domin a zamanin rayuwarsa ya yi shimfida mai kyau.
“Wadanda aka yi wa shimfidar sun zubar da shimfidar tuni saboda a yanzu idan mutum ya duba sosai zai ga cewa yankin arewacin Najeriya ya koma baya sosai don haka ne muke yin addu’ar Allah ua dauke wa yankin arewacin Najeriya masifar rashin zaman lafiya, da wannan ne muke yin fatan Allah ya sa a ci gaba da yin taro irin wannan kuma wannan kungiya da ke kokarin tunawa da marigayi Sardauna Ahmadu Bello su ci gaba da fadakar da jama’a musamman a zancen hadin kai a cire kabilanci kamar yadda su Sardauna suka yi kowa ya zauna lafiya kawai”.

About andiya

Check Also

Call Your Wife To Order, Niger Delta Groups Warn Uduaghan, Husband Of Senator Natasha

    ..Say outburst against Senate President Akpabio, shameful, unwomanly A coalition of groups from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.