….AN GANO HARAMTATTUN JAMI’O’I A NAJERIYA
A kokarin Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban Muhammadu Buhari na ganin an gyara harkokin ilimi domin a samu ilimi mai inganci ya sa hukumar da ke kula da jami’o’I ta kasa (NUC) karkashin jagorancin Farfesa Abubakar Rashid, suka gano jami’o’in da ke gudanar da harkokinsu ba bisa ka’ida ba har guda 49 da suke a wurare daban daban a fadin kasar.
Kamar dai yadda dokar Najeriya ta tanadar duk wata jami’ar da za ta fara yin karatun digiri dole ne sai Gwannatin kasar karkashin jagorancin hukumar kula da harkokin jami’o’I ta kasar ta amince ta kuma bayar da lasisi ga kowace irin jami’a ce kafin ta fara gudanar da aiki.
A bisa wannan dalili ne da hukumar kula da jami’o’in karkashin Farfesa Abubakar Rashid ke jan hankalin daukacin al’umma musamman iyayen yara dalibai da dukkan masu neman yin digiri cewa sakamakon sabawa dokar ilimi CAPE3 ta Tarayyar Nijeriya (2004).a halin yanzu duk an rufe wadannan makarantu da aka lissafa su kamar haka.
Kuma an dauki matakan ne domin Gwannatin ta jaddada kudirinta na ingantawa tare da samar da ilimi mai inganci a kasa baki daya.
Hukumar kula da jami’o’in na shawartar al’umma da su rika kula da matsayin kowace jami’a kafin su yanke hukuncin yin hulda ko fara karatu a cikin ta, domin hakan zai inganta da kuma taimakawa duk mai bukatar neman ilimin kansa ko na yayansa a koda yaushe.
Jami’o’in dai sune;
University of Accountancy and Management Studies
Christians of Charity American
University of Science and Technology
University of Industry
University of Applied Sciences and Management
Blacksmith University
Volta University College
Royal University
Atlanta University
United Christian University
United Nigeria University College
Samuel Ahmadu University
UNESCO University
Saint Augustine’s University of Technology
The International University
Columbus University
Tiu International University
Pebbles University
London External Studies
Pilgrims University
Lobi Business School
West African Christian University
Bolta University College
JBC Seminary Inc. (Wukari Jubilee University)
Kaduna illegal campus Western University
St. Andrews University College
EC-Council USA
Atlas University
Concept College/Universities (London)
Halifax Gateway University
Kingdom of Christ University
Acada University
Filfom University
Houdegbe North American University
Atlantic Intercontinental University
Open International University
Middle Belt University (North Central University)
Lead Way University
Metro University
Southend University
Olympic University
Federal College of Complementary and
Alternative Medicine
Temple University
Irish University Business School
National University of Technology
University of Accountancy and Management Studies
University of Education
Cape Coast University
African University Cooperative Development (AUCD)
Pacific Western University
Evangel University of America and Chudick Management Academic
Enugu State University of Science and Technology
Career Light Resources Centre
University of West Africa
Coastal University
Kaduna Business School
Royal University of Theology
West African Union University
Gospel Missionary Foundation (GMF), Theological University