Related Articles
Wani mai fafutukar kwato yancin jama’a dan asalin karamar hukumar Shinkafi cikin Jihar Zamfara ya lashi takobin bayyana baki dayan masu bayar da bayanan sirrin da ke karamar hukumar Shinkafi domin kowa ya san su.
Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya bayyana hakan a wajen wani taron manema labarai da ya kira a Kaduna, inda ya ce hakika ayyukan masu bayar da bayanan sirri ga yan bindiga da suke yi wa jama’ar Shinkafi ta’addanci suka kara haifarwa da kowa matsala, kasancewar shi a yanzu gidansa cike yake da yan uwa da suka yi gudun hijira daga garin Shinkafi.
Dokta Shinkafi ya ci gaba da cewa harin da yan bindigar suka kawo garin Shinkafi a wani masallaci lokacin jama’a na kokarin yin Sallar margarita ya yi sanadiyyar kashe mutane biyar wasu guda Bakwai kuma suka samu raunuka sakamakon harbin bindigar da suka samu.
Ya kara da cewa a halin yanzu a karamar hukumarsa ta Shinkafi akwai masu bayar da bayanan sirri ga yan Ta’adda a kalla mutane 84 don haka ne gamayyar kungiyoyin fafutukar kwato yancin jama’a za su Fallasa su nan ba da jimawa ba.
Dokta Shinkafi, ya bayar da bayanin irin yadda lamarin harin masallacin ya faru ga manema labarai inda ya ce “da misalin karfe Bakwai na Yammacin ranar Alhamis da ta gabata wadansu yan bindiga dauke da miyagun makamai haka kawai suka budewa mutanen da suka halarci masallacin wuta, wanda hakan nan take ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu da kuma mutane Takwas sun ji mutanan raunuka daban daban daga harbin bindiga inda nan take aka wuce da su zuwa asibiti, kuma daga nan ne wani mutum daya shima ya rasu.
Dokta Shinkafi ya kuma kara da cewa yan bindigar da ke aikin ta’addancin sun sha alwashin dawowa su lalata karamar hukumar Shinkafi, saboda sun bayyana hakan ne a cikin wata takardar da suka aikewa mutane wanda wani daga cikin shugabannin yan ta’addan mai suna Turji ya aike masu.
Dokta Shinkafi ya kuma yi bayanin cewa jita jitar da ake yadawa cewa babu wani abin da ya faru a Jihar Zamfara ba gaskiya ba ne, ya tabbatarwa da manema labarai cewa babu wani ofishin yan Sanda da aka kaiwa hari a karamar hukumar Shinkafi.
Kamar yadda ya ce, harin da aka kai ya faru ne a can karshen garin, don haka ta yaya ake yada jita jitar abin da ba haka ya faru ba. “Muna ganin dai yan Sanda sun tashi tsaye ne domin kawai su kare kawunansu sakamakon harin da aka kai masu”.
Shugaban gamayyar kungiyoyin kwato yancin jama’ar ya ci gaba da cewa duk da irin matakan tsaron da Gwamnatin Jihar Zamfara ke dauka masu muhimmanci ne, to, amma akwai bukatar Gwamnatin tarayya ta tabbatar da kawo dauki cikin gaggawa a yi amfani da karfin jami’an tsaro kamar yadda yakamata, domin shi Gwamna bashi da iko da jami’an tsaro sai Gwamnatin tarayya.
Ya kara da cewa Gwamnan Gwamnan shi ne ke da iko da jami’an tsaro ba, balantana ya ba su umarni, musamman ga jami’an Soja,yan sandan ciki da dai dukkan jami’an tsaro, wannan kowa ya san aikin shugaba Buhari ne ya bayar da umarnin don haka muke yin kira ga Buhari da ya kawo wa mutanen karamar hukumar Shinkafi da Jihar Zamfara dauki cikin gaggawa kafin su halakar da karamar hukumar baki daya.
Dokta Shinkafi ya kuma yi kira ga Gwamnati da ta hanzarta daukar matakin yin amfani da jami’an tsaron da kai domin su duk sun san wuraren da mutanen nan suke boye domin a dauki matakin karshe na ganawa da su baki daya.
“Inko ba haka ba karamar hukumar Shinkafi za ta iya kasancewa cikin wani mawuyacin hali sakamakon matsalar yan ta’addan da ke boye a cikin daji suns zuwa su na kai farmaki ha jama’ar da ba su ji ba ba su gani ba.
“Kun san a Jihar Zamfara a halin yanzu babu kayukan wayar sadarwa duk an dauke su, amma kuma yan ta’addan nan suna ta kai wa jama’a farmaki haka kawai, kuma mun san sunayen wasu daga cikin masu aikin bayar da bayanai ga yan Ta’adda kuma za mu fadi sunayensu nan ba da jimawa ba.
“ tuni min kammala gudanar da binciken mu kuma muna da hujjoji a hannu cewa suke bayar da bayanai ga yan Ta’adda”, inji shi.
Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya ce kamar ni nan “na san mutane Bakwai daga cikinsu kuma a shirye nake in Fallasa su, domin yan ta’addan na hada baki da su ne su gama da jama’armu kawai”.
Ya kuma bayyana cewa gamayyar kungiyoyin fafutukar na kokarin wani taron masu ruwa da tsaki nan ba da jimawa ba, za kuma a kira manema labarai a Fallasa sunayen masu bayar da bayanan.
“za kuma mu rubuta sunayen nasu mu mikawa Jiha da Gwamnatin tarayya domin duk ta kama su. Mun kuma dauki wannan lokacin ne domin gudanar da bincike a kansu na tsawon watanni shida da suka gabata kuma muna da tabbacin cewa lallai su na bayar da bayanan sirri ga yan bindiga masu aikin ta’addanci a cikin al’umma.
Masu wannan aikin bayar da bayanai ga yan Ta’adda su na yin rayuwa ta kasaita my da suke a cikin mu duk mun san su amma Gwamnati ba za ta iya gane su ba. Don haka dubunsu ta cika karyarsu ta kare saboda haka ni ba zan kwale su ba koda kuwa wadansu ba za su iya ba koda kuwa rayuwata za ta shiga hadari ban damu ba. Wannan aikin sadaukarwa ne domin mutane irinsu Awolowo, Zik da Sardauna duk sun yi aikin sadaukarwa ne”, inji Dokta Shinkafi Suleiman.
Game da batun idan Gwamnati taki kanawa da kuma hukunta masubayar da bayanan sirrin ga yan Ta’adda kuwa, Dokta Shinkafi ya ce ba zai yi kasa a Gwiwa ba wajen daukar matakin kai Gwamnatin tarayya da Jiha zuwa ga kotun kungiyar ECOWAS domin Kotun ta hukunta su.
Kamar yadda ya shaidawa manema labarai cewa sai da ya samu tallafi daga jami’an tsaro domin a samu fitowa da mahaifiyarsa, da yan uwansa daga Shinkafi sakamakon tabarbarewar al’amura, wanda kamar yadda ya ce a yanzu suna nan a cikin garin Kaduna sun zama yan Gudunhijira.