Home / Uncategorized / An Gano Ma’aikatan Bogi Dubu 2,363 A Jihar Zamfara 

An Gano Ma’aikatan Bogi Dubu 2,363 A Jihar Zamfara 

Gwamnatin jihar Zamfara ta bankaɗo ma’aikatan bogi 2,363 biyo bayan kammala aikin tantance ma’aikatan gwamnatin jihar.
Gwamna Lawal ya kafa kwamiti ƙarƙashin jagorancin shugaban ma’aikata na jihar a watan Agustan 2024 tare da umarnin gudanar da aikin tantance ma’aikatan jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa aikin tantancewar ya bankaɗo ƙananan yara 220 da ke karɓar albashi duk wata a matsayin ma’aikatan gwamnati.
Sanarwar ta ce, aikin tantancewar wani aiki ne da ya zama dole saboda ƙoƙarin gwamnatin jihar na aiwatar da mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000.
“Domin inganta ma’aikatan gwamnati da na gwamnatin jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya kafa wani babban kwamiti da aka forawa alhakin tantance albashin gwamnatin jihar.
“Kwamitin tantancewa ƙarƙashin jagorancin shugaban ma’aikata na jihar Zamfara, ya haɗa da Kwamishinan Kuɗi, Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Jihar Zamfara, Babban Akanta Janar, Babban Mai Al’amuran Binciken Kuɗi, Babban Jami’in Ƙididdiga a matsayin mambobi, da kuma Sakataren Zartarwa na ZITDA a matsayin sakatare.
 “Aikin farko na kwamitin ya haɗa da tabbatarwa da haɗa tsarin biyan albashi da ƙirƙirar fayil ɗin ma’aikata na yanar gizo.
“Rahoton ƙarshe da kwamitin ya miƙa wa Gwamna Dauda Lawal ya nuna cewa ma’aikata 27,109 na dindindin ne aka tabbartar da ingancinsu, yayin da ma’aikatan da ake da shakku kan aikin su sun haɗa da ma’aikatan bogi 2,363, ma’aikatan gwamnati 1082 da za su yi ritaya, 395 ma’aikatan kwangila, 261 marasa takardar shaida, 213 na hutun karatu, ƙananan yara 220 a tsarin biyan albashi da kuma mutum 67 tura su ƙaro ƙwarewa.
“Rahoton ya nuna cewa ranar ɗaukar ma’aikata 75 aiki bai yi daidai ba kuma dukkansu ƙananan yara ne lokaci guda.
“A yayin tantancewar, an fallasa ma’aikatan bogi 2,363. An biya su jimillar Naira 193,642,097.19 duk wata.
“Ma’aikata 1082 da ya kamata su yi ritaya, suna karbar jimillar kuɗi N80,542,298.26 duk wata. A lokaci guda kuma, ma’aikata biyar da aka gano sun je neman ƙwarewar aiki, ana biyansu N354,927.60 duk wata.
“Kwamitin tantancewa ya ba da shawarar dakatar da ma’aikata 207 da ba a wanke su ba. Ana biyansu jimillar albashin N16,370,645.90 duk wata.
“Kwamitin ya gano ma’aikata 12 a tsarin biyan albashi, waɗanda babu bayanansu a cikin ma’ajin bayanai amma suna karbar albashin N726,594 duk wata.
“Waɗannan tsare-tsaren tantancewa ayyuka ne na ci gaba da ƙoƙarin sa ido kan ma’aikatan Zamfara da tabbatar da gaskiya da riƙon amana a cikin ayyukan hidima wa al’umma, musamman ganin yadda za a fara biyan mafi ƙarancin albashi a watan Maris na wannan shekara.”

About andiya

Check Also

Aliko Dangote Hails IBB: ‘You’re the Architect of Private Sector in Nigeria’ 

… Donates N8bn to Presidential Library, Pledges N2bn Annually Until Completion The President and Chief …

Leave a Reply

Your email address will not be published.