Related Articles
An Kaddamar Da Sababbin Kungiyar Teloli Ta Kasa Reshen Kaduna
Mustapha Imrana Abdullahi
Kungiyar Teloli masu aikin suturar sa kowane dan Adam ke amfani da ita manya da yara har ma da Jarirai reshen Jihar Kaduna sun zabi Sababbin shugabannin da za su ja ragamar Kungiyar.
A wajen babban taron da kungiyar ta kira a Jihar Kaduna an kaddamar da sabon sunan kungiyar da ake amfani da shi a yanzu wato “Tailoring Association Of Nigeria” ( TAN) da ya maye sunan da kungiyar ke amfani da shi a can baya mai suna “National Union Of Tailoring” da yake kamanceceniya da kungiyar malamai ta kasa ( NUT).
A wajen kaddamarwar an samu halartar dimbin jama’a da suka hada tun daga yayan kungiyar da shugaban majalisar dokokin Jihar Kaduna tare da yan uwansa yan majalisa da Sarakunan gargajiya da suka hada daMadaucin Zazzau Hakimin Barnawa da wakilin mai Martaba Sarkin Zazzau kuma sauran dimbin jama’a ya siyasa kamarsu shugaban karamar hukumar Igabi honarabul Jabir Khamis Rigasa, dan majalisa daga karamar hukumar Kaduna ta Kudu Nasiru Usman mai sunan Malam da kuma dan majalisa Mista Samuel Uban Kato da suka taru suka kaddamar da karantar kungiyar.
A wajen taron dai shugaban majalisar dokokin Jihar Kaduna honarabul Ibrahim Zailani ya yi wa kungiyar Telolin kyautar filin da za su gina sakatariya inda wakilinsa ya ce amma ba maganar Sayarwa ko a ba wani ko wasu haya za a gina sakatariya ne kamar yadda aka yi nufi bayan sun zauna da shugabannin kungiyar an yi yarjejeniya a rubuce.