Home / KUNGIYOYI / An Kaddamar Da Shirin Yin Rajista Domin Bayar Da Tallafi

An Kaddamar Da Shirin Yin Rajista Domin Bayar Da Tallafi

An Kaddamar Da Shirin Yin Rajista Domin Bayar Da Tallafi
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin yin rijista don bayar da tallafi ga direbobi a jihar Katsina don rage masu radadin da wahalar da cutar Korona ta haddasa.
Karkashin hukumar kula da kanana da matsakaitan masana’antu ta Kasa (SMEDAN)
Da yake magana wajan taron wayar da kan ga masu ruwa da tsaki da suka hada da direbobin manyan motoci, da direbobin yar kurkura da masu babura wato Achaba Shugaban hukumar kula da matsakaitan sana’o’i da bunkasa su ta kasa Dokta Dikko Umar  Radda yace” mutane dubu hudu da Dari biyar za su amfana a kowace jiha.
Ya ce hakan na daga ciki shirin gwamnatin Muhammadu Buhari na tallafawa marasa karfi musamman duba da wahalar da cutar korona ta haddasa a cikin Kasar nan.
Dikko Radda ya ce” shirin ba zai yi la’akari da wani dan jam’iyya ba domin kowa zai shiga kai tsaye madamar yana da kungiyar da za ta tsaya mashi domin samun tallafin.
Kamar yadda ya ce Jihar katsina ce ta biyar a Nijeriya wajan yawan mutanen da suka shiga shirye shiryen Gwamnati na tallafawa masu kananan sana’oi a kasar nan sanadiyyar maida hankali da mahukunta suka yi wajan wayar da kan al’umma.
Shima a nashi jawabin mai ba Gwamnan Jihar katsina shawara a kan bunkasa sana’oi da zuba hannun jari Alh Ibrahim Tukur jikamshi, cewa ya yi ” jihar katsina ta dauki matakan wayar da kan al’ummma a kan irin wadannan shirye shirye don ci gaban jihar.
Taron dai ya samu halartar shuwagabannin kungiyoyin direbobin hanya dana keke Napep da masu babur wato yan Achaba da sauransu.

About andiya

Check Also

Muna Kokarin Kafa Hukumar Da Za Ta Hada Hukumomi Wuri Daya Ne – Honarabul Gumi

Bashir Bello majalisa Abuja Honarabul Suleiman Abubakar Gumi wakilin kananan hukumomin Gumi da Bukkum a …

Leave a Reply

Your email address will not be published.