Home / Kasuwanci / AN KADDAMAR DA TAKIN ZAMANI NA DANGOTE

AN KADDAMAR DA TAKIN ZAMANI NA DANGOTE

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
An bayyana kamfanin Dangote a matsayin katafaren kamfanin da ke kokarin bunkasa harkokin Noma a Najeriya, Afrika da duniya baki daya.
Injiniya Dokta Mansir Ahmad ne ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da Takin Zamani na Uriya wanda kamfanin Dangote ya samar domin ci gaban manoma da kasa baki daya.
Injiniya Mansir Ahmad, wanda ya kaddamar da Takin Zamanin a madadin kamfanin Dangote, domin manoma su samu damar ci gaba da amfani da shi a wajen Noman rani da na Damina.
“Hakika babban abin da wannan kamfanin ya Sanya a gaba shi ne bunkasa harkokin Noma da sauran dukkan bangarorin kasuwanci  a kasa baki daya.
An kuma tabbatar da cewa ana kai Takin Zamani na Dangote zuwa wadansu kasashe na duniya, kuma hakan ya faru ne sakamakon irin ingancin da Takin yake da shi.
An ci gaba da cewa an samar da Takin zamanin Dangote ne bayan gudanar da kyakkyawan bincike domin samun inganci da yanayin kasar Noma ta hanyar yin amfani da Kimiyyar zamani don haka duk wanda ya yi amfani da Takin zai samu biyan bukata.
Injiniya Mansir Ahmad ya kuma yabawa masu shirya kasuwar duniya ta kasa da kasa da ke Kaduna bisa damar da suka ba kamfanin Dangote ya kaddamar da Takin zamaninsu a hukumance domin hakan shi ne na farko, “saboda an fara yin sa ne watanni shida ko Bakwai da suka gabata”, inji Mansir Ahmad.
Mansir Ahmad ya kuma tabbatarwa manema labarai cewa katafariyar matatar mai ta Dangote za ta rika samar da miliyoyin litar mai da zai wadanci kasar nan, kuma mai mai matukar inganci saboda ko a kasashen turawa na tarayyar Turai aka kai man za a iya sayar da shi domin ingancinsa daya ne da na man kasashen tarayyar Turai.
Injiniya Mansir Ahmad ya kuma bayyana cewa nan gaba kadan kamfanin Dangote zai kara samar da wadansu abubuwan da jama’a za su ci gaba da yin amfani da su, kamar Man fetur da dangoginsa da kuma mota kirar kamfani da sauran abubuwa da dama kasancewar kamfanin na kokarin samar da sababbin abubuwan amfanin jama’a a koda yaushe.
Kamfanin Dangote na yin Suga,Magi,Gishiri,Sumunti da sauran kayan dandanon abinci kala kala, kuma nan gaba za su ci gaba da samar da wadansu kayayyakin da dama.
A waje daya kuma manoma sun yabawa kamfanin Dangote bisa irin kokarin kara habbaka harkokin Noman da yake yi, wanda hakan ke ba su damar ci gaba da fadada harkokin Nomansu.
“Hatta da farashin Takin zamani a shekarar da ta gabata Takin Yuriya na kamfanin Dangote ne ya cece manoman Najeriya kowa ya samu yin Noma a cikin sauki da kwanciyar hankali”, inji Manoma.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.