Home / Labarai / An Kama Mutane Uku Da Ke Yada Bayanan Karya A Kaduna

An Kama Mutane Uku Da Ke Yada Bayanan Karya A Kaduna

An Kama Mutane Uku Da Ke Yada Bayanan Karya A Kaduna
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin kwamishinan kula da harkokin tsaro da al’amuran cikin gida Malam Samuel Aruwan sun yi nasarar kama wadansu mutane uku da suke yada bayanan karya wai za a kai hari a wani¬† kauye
Wadansu mabiya addinin Kirista da ke a kauyen Unguwar Kwaki, a karamar hukumar Jema’a cikin Jihar Kaduna sun tabbatar da cewa an kirasu a wayar hannu ta ta fi da gidanka inda wasu mutane suke bayyana masu cewa su Fulani ne saboda haka suna gaya masu cewa su tsammaci kai masu hari a yan kwanaki masu zuwa tun daga lokacin da suka kirasu a wayar.
Wannan lamari dai na kiransu a waya ya haifar masu da tsaro tare da tsananin fargabar da ta haifar masu da yin hijira daga wurin da suke inda Mata da yara suka Tsere daga garin da suke.
Nan da nan hukumomi da suka hada da sojoji sai suka shiga aikin tattara bayanai, kuma sun yi nasarar kama wadannan mutanen a kauyen Sabon Kaura da ke Karamar hukumar Zangon Kataf a Kudancin Kaduna, da suka fake da cewa su makiyaya ne. Su dai yaran guda biyu masu sunaye Lamar haka Joel Luka, Emmanuel Daniel da Sylvester Daniel, duk sun amsa laifin aikata wannan yada Jita jitar.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.