Home / Labarai / AN KAMMALA SHIRIN FARA TATTAUNA AL’AMURAN TSARO TSAKANIN NIJAR DA NAJERIYA A KATSINA

AN KAMMALA SHIRIN FARA TATTAUNA AL’AMURAN TSARO TSAKANIN NIJAR DA NAJERIYA A KATSINA

DAGA IMRANA ABDULLAHI 
A kokarin ganin an samar da ingantaccen tsarin kula da tsaron lafiya da dukiyar jama’ar kasashen Najeriya da Janhuriyar Nijar a halin yanzu kasashen biyu suka shirya wani gagarumin taron tattauna batutuwan tsaro domin samawa al’ummar kasashen biyu da nufin samo mafita.
Taron da za a yi a ranar gobe Talata, Gwamnan Jihar Katsina ne Alhaji Aminu Bello Masari ke karbar bakuncin taron da ake saran zai gudana a birnin Katsina.
Gwamnatin Jihar Zamfara ta aike da wata babbar tawagar da ke wakiltar Jihar karkashin jagorancin mataimakin Gwamnan Jihar Sanata Hassan Nasiha da kuma sakataren Gwannatin Jihar Alhaji Dokta Kabir, sai kuma Jihohin Sakkwato, Kebbi da Jihar Maradi,Doso da dai sauran wuraren da ke da iyakar da ake kokarin tattaunawa da su a lokacin taron.
Kuma kamar yadda majiyar mu ta sanar cewa za a fitar da bayanin bayan taro kuma za a sanar da inda taron na gaba zai gudana a tsakanin Jihohin da suka halarci taron.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.