Home / Labarai / Lalacewar Darajar Naira: A Cire Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Emefiele – Kailani

Lalacewar Darajar Naira: A Cire Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Emefiele – Kailani

Sakamakon irin tsananin damuwar da yan Najeriya suka shiga biyo bayan koma bayan da aka samu na lalacewar darajar kudin Naira ya sa wasu daga cikin kasar na kiraye kirayen a cire Gwamnan Babban Bankin kasa, Mista Godwin Emefiele daga shugabancin Bankin.
Shugaban wata babbar kungiyar da ke kokarin ilmantar da jama’a kan al’amuran zabe da wayar da kan yan kasa Injiniya Kailani Muhammad ne ya yi wannan kiran a wajen wani taron manema labarai a Kaduna.
Kamar yadda kungiyar ta ce, Emefiele ya kasa nuna kwarewa tare da kawo al’amuran da kasar za ta ci gaba musamman ta fuskar tattalin arzikin kasa, saboda haka kudin naira da ake amfani da su a tarayyar Najeriya sai lalacewa suke yi a kullum kwana, wanda sanadiyyar hakan mutane masu karamin karfi ke shiga cikin wani mawuyacin hali.
Sai Injiniya Kailani, ya kara karfafa cewa ya dace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cire shi daga matsayin shugabancin Babban Bankin na Najeriya, domin dukkan alamu sun tabbatar da gazawar Emefiele na ya ci gaba da jagorantar Bankin.
Da yake jawabi a game da batun wayar wa da jama’a kai a zaben shekarar 2023 mai zuwa, Injiniya Kailani ya ce alamun da kowane dan Najeriya ke da su na tabbatar da cewa Godwin Emefiele ya kasa lalubo makamar da za a samu wata nasarar hana lalacewa da koma bayan kudin takardar naira.
Kailani ya kuma bayyana bacin ransa a kan irin yadda shugaban Bankin na Najeriya ya kasa yin wani katabus a game da ceton rayuwar masu karamin karfi take a cikin kasar.
“Kamar yadda ya ce ba abin da za a iya dogaro da shi ba ne cewa farashin kudin dala a wajen Gwamnati ya zama naira dari hudu (400) a kan dala daya, amma kuma a kasuwar bayan fage har ta na kai wa naira dari Bakwai (700) da a yanzu lamarin farashin ma ya doshi naira dubu daya a kasuwar bayan fage.
Injiniya Kailani ya kuma ya ba wa yan majalisar Dattawa a kan irin kokarin da suke yi na samar da mafita; “Hakika wannan abin murna ne da farin ciki yadda yan majalisar Dattawa suka fara daukar matakan ragewa Gwamnan Babban Bankin kasar karfin da yake da shi musamman irin yadda suke kokarin duba dokar da ta kafa Babban Bankin kasa CBN
“A madadin sama wa kudin Najeriya daraja sai Gwamnan Babban Bankin ya buge da kokarin tsunduma cikin harkokin siyasa ya na neman zama dan takarar shugaban kasa ba tare da yin la’akari da irin abin da ke gabansa ba na shugabancin Bankin Najeriya”.

About andiya

Check Also

PRESIDENT TINUBU COMMENDS DANGOTE GROUP OVER NEW GANTRY PRICE OF DIESEL

  President Bola Tinubu commends the enterprising feat of Dangote Oil and Gas Limited in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.