Home / News / An Kammala Tiruna Kilomita 1,536 A Jihar Jigawa – Aminu Usman

An Kammala Tiruna Kilomita 1,536 A Jihar Jigawa – Aminu Usman

Mustapha Imrana Abdullahi

wamnatin Jihar Jigawa ya zuwa yanzu ta kammala gina hanyoyi sababbi da tsofaffi wadanda tsohuwar gwamnatin jam’iyyar PDP ta fara amma ba ta kammala su ba, da kuma sababbi wadanda gwamnatin jam’iyyar APC a karkashin jagorancin gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ta fara a duk fadin Jihar domin inganta sha’anin zirga-zirga da walwalar jama’a wadanda yawan su ya kai tsawon kilomita 1,536 .

Kwamishinan ma’aikatar ayyuka da sha’anin sufuri na Jihar Jigawa, Injiniya Aminu Usman ne ya bayyana haka, a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a Kaduna inda ya halarci taron bita wanda gwamnatin Jihar ta shirya na kwanaki biyu domin koyar da manyan ma’aikatan gwamnatin Jihar tare da masu rike da mukaman siyasa, musamman masu ba gwamna shawara domin Sanin sabbin dabarun Makamar aiki .

Ya ce a lokacin da suka zo waccan tsohuwar gwamnatin karkashin PDP ta bayar da aikin kwangilar gina hanyoyi har 716 wanda ya zuwa yanzu gwamnatin nan ta kusan kammala su abin da ya yi saura ba su wuce guda hamsin ba gaba daya,sannan ga sababbin da ya ce sun yi wanda tun da farko ya ce gabadaya sun kai  tsawon kilomita 1,536 .

Dangane da taron bitar da suka zo yi a Kaduna kuwa kwamishinan ayyuka da sufurin ya ce taron ya kara koyar da su sabbin dabarun tafiyar da aiki bisa tsarin doka da kuma kiyaye amana,sa’annan kuma kowa ya san iyakan shi, wani baya shiga aikin want .

Haka ya cr a karshe dai burin wannan gwamnatin ne ta yi wa al’amurar jihar aiki domin inganta rayuwar su, da bunkasa martaba da tattalin arzikin Jihar Jigawa

About andiya

Check Also

Majalisar Wakilai: Sani Jaji Zai Maye Gurbin Abbas Tajuddeen?

Daga Imrana Abdullahi Kamar yadda wadansu bayanai suka bayyana a kafar yada labarai ta jaridar …

Leave a Reply

Your email address will not be published.