Home / News / An Kashe Mutum 7, Shanu 712 Da Tumaki 138 – Miyatti Allah

An Kashe Mutum 7, Shanu 712 Da Tumaki 138 – Miyatti Allah

An Kashe Mutum 7, Shanu 712 Da Tumaki 138 – Miyatti Allah
Mustapha Imrana Abdullahi
Shugabannin kungiyar Fulani ta Miyatti Allah ta kasa reshen Jihar Kaduna karkashin jagorancin Haruna Usman Tugga, sun bayyana cewa duk da irin kokarin da suke yi domin ganin an samu zaman lafiya tsakanin al’ummar Fulani da Atyap a kowane yanki sai gashi a kwanan nan an kashe masu mutane 7, Shanu dari 712 da kuma Tumaki 138 a yankin Gora Gan da ke Kudancin Kaduna.
Mun samu wannan asarar ne a cikin kwanakin sati daya kacal.
A cikin wata takardar da suka karantawa manema labarai a Kaduna mai dauke da sa hannun Haruna Usman Tugga shugaban kungiyar Miyatti Allah, Musa Muhd Gambo Sakataren kungiyar da kuma Ibrahim Bayero Zango Daraktan yada labarai na kungiyar a kaduna.
Sun bayyana cewa suna kira ga shugabannin al’ummar Atyap da su rika aiwatar da tsare tsaren zaman lafiya da rungumar Juna da ake ta aikin fadakar da jama’a domin samun ci gaba.
Sun shaidawa manema labarai a Kaduna cewa a koda yaushe suna mamakin irin yadda ake kashe mutanen su tare da lalata masu Dukiya da kuma kisan dabbobi ba gaira ba dalili.
Sun tabbatarwa manema labarai cewa su ne zargin cewa an shirya kashe Mutanensu ne kawai kuma hakan ya faru a yankin Atyap a Gora Gan da ke Gundumar Gora a yankin masarautar Atyap, kuma an kashe wani shugaban al’ummar Fulani a yankin Auchau lokacin da ya dawo daga wajen yin taron zaman lafiya da aka shirya a yankin Atyap amma madadin zaman lafiya sai aka kare da rasa ran Ardon Fulanin da ya halarci taron zaman lafiyar.
Sun bayyana mutanen da suka rasa rayukan na su kamar haka wakilin Fulani na masarautar Atyap, Wakili Ardo Pate Kurmi shekarunsa 51 sai 2 Ardo Muhammad Anchau shekarunsa 55 3 Muhammad Yakubu shekarunsa 41, sai 4 Mustapha Bako shekaru 12 sai  5 Yusuf Hamidu shekaru 14, 6 Yakubu Aruwa shekarunsa 25 sai 7 Ibrahim Yuguda shekaru 30.
Shugabannin kungiyar Miyatti Allah sun fito fili sun nemi da a biya diyyar wadannan dukiyar Dabbobin da aka rasa, kasancewar an cuci masu wadannan dabbobin kasancewar a yanzu wasu ba su da komai.
Shugabannin kungiyar sun kuma zargi wani tsohon Soja da ya ajiye aiki mai suna Iko Ibrahim da cewa ya handame babban Gandun da Gwamnatin Jihar Kaduna ta ware tun tali tali domin kiwon Dabbobi amma a yanzu ya je ya killace fili mai yawan hekta dubu 30,000 a matsayin Gonarsa.
Kamar yadda shugabannin Fulanin suka bayyana ta bakin mai magana da yawun kungiyar Bayero Ibrahim Zango cewa shi wannan tsohon Sojan na hada baki da wasu jami’an sojojin da aka kai aikin tabbatar da tsaro a yankin na Kagarko amma sai shi tsohon sojan ya rika amfani da su ta hannun wani jami’in tsaro ma’aikacinsa su na kafa shingaye a yankin su na shiga cikin Gandun dajin da aka ware domin kiwon Dabbobin.
” Su na cin mutunci tare da tsoratar da Fulani a wannan wuri da sunan wai wurinsa Gonarsa ce ne, domin ya yi gine gine a cikin Gonar inda har ya gina manya manyan wuraren ajiya”, inji Bayero Ibrahim Zango.
Muna dai yin kira ga daukacin al’ummar Fulani da su ci gaba da zama lafiya tare da kokarin kiyaye doka da oda a duk inda suke a bari hukuma ta yi aikinta.

About andiya

Check Also

Northern Christian Leaders Pay Homage to Khalifah Sanusi, Strengthening Ties.

Northern Nigerian Christian Clerics Pay Homage to His Highness Khalifah Sanusi Lamido Sanusi to Strengthen …

Leave a Reply

Your email address will not be published.