Home / Labarai / An Kashe Tsohon Dan jarida Hamisu Danjibga A Gusau

An Kashe Tsohon Dan jarida Hamisu Danjibga A Gusau

Daga Imrana Abdullahi

Bayanan da muke samu daga Jihar Zamfara na cewa wadansu mutane da ya zuwa yanzu ba a san ko su waye ba sun kashe tsohon dan jarida a Jihar Zamfara Malam Hamisu Danjibga.

Kafin mutuwarsa dai ya yi aiki da kafafen yada labarai da dama da suka hada da Muyar Najeriya, Jaridar Gamzaki ya na kuma aikawa rediyon Vision Fm labarai
Kuma Iyalansa sun yi shelar bacewarsa kwanaki biyu bayan tafiya Sallar Asuba tun daga nan sai dai wannan mugun labarin kawai aka ji.
Kuma sanannen mutum ne a fagen buga waya domin bayar da gudunmawarsa a kafar yada labarai ta rediyon tarayya FRCN
Kamar yadda muka samu bayani an dai samu gawarsa ne a bayan gidansa da ke Unguwar Samaru cikin garin Gusau a karamar hukumar Gusau babban birnin Jihar Zamfara.

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.