Home / Labarai / An Mayar Da Dokar Hana Fita A Kaduna Daga 6 Zuwa 6 Na Yamma

An Mayar Da Dokar Hana Fita A Kaduna Daga 6 Zuwa 6 Na Yamma

An Mayar Da Dokar Hana Fita A Kaduna Daga 6 Zuwa 6 Na Yamma
Imrana Andullahi
Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru ta mayar da dokar hana fita a daukacin kananan hukumomi 23 daga karfe shida na Asuba zuwa shida na Yamma.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa ta duba sosai ta kuma mayar da dokar hana fita da ta Sanya daga karfe shida (6) na Asuba zuwa shaida (6) na Yamma a baki dayan kananan hukumomi 23 da ke fadin Jihar baki daya.
Bayanin hakan ma kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan kula da tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna Malam Samuel Aruwan Aruwan Sanya wa hannu.
Sanarwar ta ci gaba da cewa daga yau ranar Alhamis 29 ha watan Okutoba, 2020, dukkan jama’ar Jihar na da yancin gudanar da harkokinsu daga karfe 6 na Asuba zuwa karfe 6 na Yamma.
Amma sanarwar ta yi bayani karara cewa an hana zirga zirga a lokacin da dokar ta fara bayan shida na Yamma wato cikin Dare kenan.
Gwamnatin ta kuma yi kira ga daukacin jama’ar Jihar Jihar su ci gaba da kulawa sosai domin kai rahoton duk wani al’amarin da ba su amince da shi ba domin jami’an tsaro su dauki matakin da ya dace.

About andiya

Check Also

DOLE SAI MUN SANYA FASAHAR ZAMANI DON YAƘI DA MATSALAR TSARO -GWAMNA LAWAL GA MAJALISAR ƊINKIN DUNIYA

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada buƙatar amfani da manyan na’urorin zamani domin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.