Sakamakon kokari jajircewa da aiki tukuru tare da yin amfani da abin hannunsa ba da gajiyawa ya sa mutumin da ke yin takarar Kujerar dan majalisar wakilai ta tarayya daga mazabar Shinkafi da Zurmi, honarabul Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, Sarkin Shanun Shinkafi na farko ya nada Abubakar Lauwali Kaura Shinkafi a matsayin babban jagoran tafiyarsa domin a cimma nasarar da ake bukatar samu na zuwa majalisar Abuja ya wakilci kananan hukumomin Zurmi da Shinkafi a bangaren yada bayanai da manufofin tafiyar a dandalin Sada Zumunta na zamani da ake kira ( Social media team).
Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya bayyana hakan ne a lokacin da Abubakar Lauwali Shinkafi ya dauko wata tawagar jajirtattuna mutanen da suka hada da zaratan matasa da Dattawa a wadannan kananan hukumomin tun daga Jihar Zamfara suka kawo ziyarar ban girma tare da goyon baya ga Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi a gidansa da ke cikin garin Kaduna.
Kamar dai yadda muka ambata a can baya sakamakon irin kokari da jajircewar Abubakar Lauwali Shinkafi, ya sa mai neman kujerar Dokta Suleiman Shinkafi ya ambata da bakinsa cewa ya ba Abubakar Lauwali Kaura ko-odinetan tafiyar da domin a samu kwalliya ta biya kudin sabulu, kasancewar Dokta Suleiman mutum ne na kowa.
Kuma.kamar yadda za ku iya gani a wannan hoton ga shi nan lokacin da dan takara Suleiman Shu’aibu ke mikawa Abubakar Lauwali takardar kama aiki a matsayin ko- odinetan tafiyar da babu tantama za a samu nasarar da ikon Allah.
Ga dai irin yadda babban taron ziyarar ya kasance nan a wani taron da aka yi a dakin taro na gudan tunawa da marigayi Sardauna Sa. Ahmadu Bello da ke Kaduna.
Abubakar Lauwali Kaura Shinkafi, shugaban tafiyar Sarkin shanu na farko Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi
Sani Muhammad Shinkafi, kamar yadda kowa ya Sani ba mai kishin wannan bawan Allah da ya rungumi jama’a da ci gaban jam’iyya
“Akwai lokacin da ya raba Injunan Nika ga mata da ake yin Nika da su a halin yanzu a cikin gida je da motoci ga jama’a, abin da ya rage shi ne kowa ya tabbatar da zuwa gida gida sako sako ya tallata Sarkin Shanu ga al’umma domin a samu nasarar da kowa ke bukata
Ubaida Idris Zurmi, ni a hakika ina zaune a Jihar Zamfara ban taba ganin Sarkin Shanu ba amma ina jin abin da yake yi wa jama’a hakika ina son in gan shi domin ya taimaki jama’ar mu kwarai”,
Hamisu Umar Zurmi, tsohon yaron Bello Hassan kowa ya Sani ba shi da Yaro a Zurmi kamar ni ko da ba ko sisi muna tare da shi.
” kai an kai lokacin da duk shiyyar mu ba wanda ke Bello Hassan sai ni kadai kuma muna ta Gwagwarmaya har Bello Hassan ya ci zabe sakamakon hakan ya yi Mani alkawarin za a yi tafiya tare da ni ko ina har rike hannu na ya yi cewa zai ta fi tare da ni”.
“Kai har rufe ni aka yi saboda harkar siyasa na kai shekara 15 a PDP ba a min komai ba, amma da na dawo APC hakika an taimake ni na kuma samu baiwa sosai”.
“Ina son la rike mu Amana a cikin harkar siyasa, koda yake ina kiran ruwa, fatar mu a rike mu Amana fatar mu dai in na ce ina yi to ko rayuwata ina iya bayarwa”.
Sai tsohon Kantoman karamar hukumar Shinkafi, Honarabul Bashar Shinkafi, hakika wannan kanin na mu mutum ne mai tabbaci kuma ni tun 1990 aka zabe ni shugaban karamar hukuma shekaru 35 da suka gabata, in ban taba ganin abin da Dokta Suleiman ya yi
“Tun a lokacin da akwai wadansu mutane da sun kai Goma (10) ana hade a duk Shinkafi, ko auren fari ban yi ba amma sai ga ni ni ne shugaban karamar hukuma, tun a lokacin Marafa na ce masa ina son ka hada ni da Sarkin Shanu, mu da ake karawa tsawo da tsawon iyaye da sauran duk wata dama sai ga Sarkin shanun Shinkafi na farko ya zama ya yi fice kuma ko a yanzu ya na nan har yanzu duniya na nan ta na tare da shi.
Yusuf Wazof cewa ya yi, ” Tun lokacin Namadi Sambo na Gwamnan Jihar Kaduna Yakowa na mataimakin Gwamna ne Sarkin Shanun Shinkafi na farko ya saka mu cikin gidan gwamnati ya gabatar da kasida ya kuma Karrama gwamna, ni a matsayi na sai da na ji wani shauki shin wai ni ne kuwa a wannan wurin cikin gidan Gwamnatin kaduna?
“Ko a lokacin da muka zagaya Jihohi 19 sai da muka yi kamfe ko ina.
Sa’adiyya Sani Shinkafi, addu’a ta yi cewa Allah ya kara taimakawa jama’ar wannan mazaba ta Shinkafi da Zurmi.
Hamza Na Makka Zurmi ko wadanda ba su nan hakika sun ce a gaya wa jama’a cewa suna tare da wannan tafiya kuma ina tabbatar maka cewa baka ga yada manufa ba sai yanzu zaka ga wannan kokari na mu za mu yi tafiyar tsakani da Allah a matsayina na shugaban soshiyal midiya na karamar hukumar Zurmi.
Aminu Ibrahim Shinkafi, ya mu goyi bayan wannan tafiyar tsakani da Allah domin mun yi tafiya amma ba mu ji dadin tafiyar da muka yi bamu ji dadin ta ba.
Ina kira ga jama’a da a cire Kwadayi kowa ya yi mutum ba tare da yin Kwadayi da son zuciya ba, ina tabbatar maku za a yi Gwagwarmaya a halin yanzu
Husaini Usman Zurmi, Allah kara mu cikin jindadi mu samu nasarar wannan tafiya ta Jirgin tsira Jirgin Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi Sarkin shanun Shinkafi na farko ceto kowa ya ji dadi.
Iliyasu Aliyu, haifaffen Shinkafi domin Mahaifina ya yi aikin Banki a Shinkafi don haka mu a Shinkafi aka haife mu, kasancewar muna tare da jagoran tafiyar nan Abubakar Lauwali Shinakfi muna tare da shi duk da mu asalin mu mutanen Adamawa ne duk inda za a shiga zan shiga game da wannan tafiyar