Home / Kasuwanci / An Rantsar Da Ishaya Idi Sabon Shugaban Kasuwar Duniya Ta Kaduna

An Rantsar Da Ishaya Idi Sabon Shugaban Kasuwar Duniya Ta Kaduna

 

Daga Imrana Abdullahi
A kokarin ganin al’amura sun ci gaba da tafiya kamar yadda ya dace hakan ta Sanya aka gudanar da zaben sababbin shugabannin da za su ci gaba da jan ragamar tafiyar da kasuwar duniyar kasa da kasa da ke garin Kaduna karkashin jagorancin Mista Ishaya Idi, da dukkan mukarraban da za su ja ragamar shugabancin kasuwar.
Da yake gabatar da jawabinsa a wajen taron shugaban kwamitin Amintattun kasuwar duniyar Madakin Zazzau Alhaji Muhammadu Munnir Jafaru, cewa ya yi bai ji dadi ba da irin yadda ya ga halin da kasuwar take ciki musamman harabar da ke cike da ciyawa ba tare da an yi gyara ba.
Mista Ishaya Idi kenan a cikin farin kaya yake karbar rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Kasuwar duniya ta Kaduna wanda Barista Edoh Baba ya Rantsar
Munnir Jafaru wanda shi ne kuma Uba na wannan Kasuwar duniyar kasa da kasa, a ranar Asabar da ta gabata a wajen taron rantsuwa da kuma kaddamar da shugabannin da za su ja ragamar kasuwar karkashin jagorancin Ishaya Idi, ya ce hakika ana da kyau kwarai matuka shugaban ya rika tambaya tare da yin aiki tare da sababbi da tsofaffin shugabannin wannan kasuwa domin samun shawara mai kyau da ta dace ta yadda za a ci gaba da samun ci gaban da ya dace a kasa baki daya.
” Hakika wannan harabar kasuwar na bukatar a yi mata gyara na musamman domin akwai gyare – gyare kwarai ta yadda za ta yi dadin kallo sosai ko a idanu ma idan an zo wurin, kamar dai yadda darajar kasuwar take a da can “, inji Madakin Zazzau.
Ya kuma bayar da shawara a kan bukatar da ke akwai na yin amfani da harabobin da ke kasuwar a koda yaushe ba wai sai lokacin cin kasuwar duniya ba kawai.
Sai Madakin Zazzau ya shawarci ainihin sababbin shugabannin da su yi aiki tare da cika alkawarin da suka dauka domin Allah ne shaida kuma ya na kallon kowa a koda yaushe.
Ya kuma yi godiya tare da yin jinjina a game da irin yadda aka gudanar da zaben shekara shekara na kasuwar da aka yi a ranar 25 ga watan Nuwamba na shekarar 2023.
Da yake nasa jawabin sabon zababben shugaban kasuwar duniyar kasa da kasa da ke Kaduna Mista Ishaya Idi cewa ya yi zai ci gaba da aiwatar da ayyukan da aka san shi ya na aikatawa domin samun ciyar da tattalin arzikin Jihar Kaduna da kasa baki daya gaba.
“Za mu yi tafiya tare da kowa a koda yaushe ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu
Sauran wadanda aka Rantsar sun hada da Alhaji Faruk Suleiman da kuma Alhaji Suleiman Aliyu da dai sauran yan  hukumar gudanarwar kasuwar da dama.
Wanda ya Rantsar da su shi ne Barista Edoh Baba Abicheh
Babban Sakatare a ma’aikatar kula da harkokin Kasuwanci da kirkire – kirkire Dokta Ya’u Sale Auchan ne ya wakilci kwamishinan ma’aikatar inda Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi godiya kwarai wajen ganin yadda aka gudanar da zaben shugaban cikin kwanciyar hankali da lumana da kuma girmama Juna abin da suka ce babbar nasara ce ga Jihar da al’ummar kasa baki daya.
Kuma Ya’u Sale Anchau ya ci gaba da bayanin cewa ana saran a zamanin wannan shugabanci da aka Rantsar za a samu bunkasar harkokin kasuwanci a koda yaushe.

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.