Home / KUNGIYOYI / An Rantsar Da Karrama Shugabanni, Jagororin Kungiyar NASWDEN A Kaduna

An Rantsar Da Karrama Shugabanni, Jagororin Kungiyar NASWDEN A Kaduna

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna

Dokta Mubarak Labaran Liman, mukaddadhin shugaban kungiyar NASWDEN ne na kasa, ya yi kira ga daukacin yayan kungiyar da su ci gaba da yin hadin kai da kokari a tafiyar da kungiyar gaba tare da taimakon Juna.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron da kungiyar ta yi a Kaduna.

Dokta Mubarak Labaran Liman ya kuma mika sako ga al’umma da kuma Gwamnati inda ya yi kira da a ci gaba da ba yayan kungiyar hadin kai a kuma ci gaba da ba su tallafi ta yadda yayan kungiyar za su kara zage dange wajen samar da taimako ga al’umma aikin yi da tsaftace muhalli da nufin ciyar da sanar gaba a kan batun sarrafa shara ta zama abin yin amfani a koda yaushe a duk fadin kasar nan mai albarka.

Muna kuma yi wa Allah godiya da aka samu yin wannan taron lafiya aka kammala lafiya har aka kaddamar tare da Rantsar da sababbin shugabanni na Jihar Kaduna kuma aka bayar da lambobin Yabo ga wasu mambobin jiha da ma wasu na wasu a mataki na kasa sakamakon irin kokarin da suka yi wa kungiya da tafiyar da sanar nan.

Barista Usman Salisu Jundullahi ne ya Rantsar da sababbin shugabannin na Jihar Kaduna da kuma na yankin arewacin Najeriya da suka hada da Abuja.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.