Home / Labarai / An Sace Wani Malamin Addinin Kirista A Jema’a

An Sace Wani Malamin Addinin Kirista A Jema’a

An Sace Wani Malamin Addinin Kirista A Jema’a
Mustapha Imrana Abdullahi
Jami’an tsaro sun kawo wa Gwamnatin Jihar Kaduna rahoton sace wani Malamin addinin Kirista mai suna Emmanuel Egoh Bako tare da matarsa Cindy Bako a karamar hukumar Jema’a.
Bayanin hakan na cikin wata takardar sanarwa da ke dauke da sa hannun kwamishinan kula da harkokin tsaro da al’amuran cikin gida Malam Samuel Aruwan.
Kamar yadda takardar ta bayyana wadansu mutane ne da ba a san ko su waye ba suka kaiwa wurin Ibada na Albarka da ke kan titin  Fadan Kagoma kwoi hari.
Nan da nan suka rika yin harbin kan mai uwa da wabi inda suka samu wata mota kamar yadda zaku iya gani a wannan hoton da ke cikin labarin.
Sannan suka sace wannan Malamin addinin Kirista Bako da mai Dakinsa ( matarsa), Douglas.
Wadansu jami’an tsaro sun yi Sauri sun Isa wurin sun kuma dauki matakin mayar da martani, amma dai yan bindigar sun tsere da wadanda suka sace din.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.