Home / Labarai / An Sako Dalibai 5 Daga Cikin 39 Da Aka Sace A Kaduna

An Sako Dalibai 5 Daga Cikin 39 Da Aka Sace A Kaduna

An Sako Dalibai 5 Daga Cikin 39 Da Aka Sace A Kaduna
Imarana Abdullahi
Dalibai biyar daga cikin jimillar  guda 39 da aka sace aka kuma yi Garkuwa da su a halin yanzu sun samu kubuta daga yan bindigar.
Daliban na makarantar koyon aikin Gona da Gandun daji da ke Afaka su biyar suna hannun sojoji ana duba lafiyarsu.
Duk wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwar da aka rabawa manema labarai da ke dauke da sa hannun kwamishinan ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna Malam Samuel Aruwan.
Takardar ta ci gaba da bayanin cewa rundunar sojan Nijeriya sun shaida wa Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru El- Rufa’i cewa guda biyar (5) colin daliban makarantar koyon aikin Gona da ke Afaka, an sako su da Yammacin yau Litinin kuma su na nan ana kokarin duba lafiyarsu.
Kuma nan gaba Gwamnatin Jihar Kaduna za ta ci gaba da sanar wa da jama’a halin da ake ciki a game da lamarin

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.