Home / Labarai / AN TUBE RAWANIN YAKUBU DOGARA A BAUCHI

AN TUBE RAWANIN YAKUBU DOGARA A BAUCHI

Masarautar Bauchi ta dakatar da sarautar da ta ba tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Yakubu Dogara, a matsayin Jakadan Bauchi.
Yakubu Dogara dai ya wakilci al’ummar kananan hukumomin Dass, Tafawa Balewa Da Bogoro duk a Jihar Bauchi.
Masarautar dai ta dauki matakin ne saboda wasu rikice-rikice da aka samu a Kananan Hukumomin Tafawa Balewa da Bogoro a ’yan kwanakin baya.
Da yake yi wa manema labarai jawabi a Bauchi, Galadiman Bauchi kuma Hakimin Zungur, Sa’idu Ibrahim Jahun, ya ce, “Masarauta ta yanke shawarar jingine sarautar har sai kotu ta yanke hukunci a kan lamarin.
Wannan hoton ne ke nuna lokacin da masarautar ke yi wa manema labarai jawabi
“Idan za a iya tunawa, a ranar hudu ga watan Janairun 2022, masarauta ta bayyana matsayinta a kan rikice-rikicen da aka samu a Tafawa Balewa da Bogoro a ranakun 30 da 31 ga watan Disamban 2021.
“Mun yi Allah wadai da wannan rikicin, wanda abin takaici ne, kuma muna kira ga gwamnati da ta binciki lamarin sannan ta hukunta duk mai hannu a cikinsa.
“A taron Majalisar Masarauta na kwanan nan, mun duba lamarin tare da yin mamakin yadda mai rike da sarauta za a same shi da hannu dumu-dumu a ciki.
“Abin takaicin shi ne bai nuna wata alamar nadama ko tausayi ba ga abin da ya faru da masu martaba Sarakunan Bauchi da Dass.
“Rikicin ya raba kan Sayawa, masu goyon baya da masu adawa.
Tsohon Kakaki Yakubu Dogara ya rubuta wasika zuwa ga Babban Sufeton ’Yan Sanda yana ba da shawarar a dage bikin, yana ikirarin an ware wasu masu fada a ji a yankin, sannan ya yi gargadin cewa za’a iya samun rikici in aka yi a hakan.
“A sakamakon haka, an kai wa saraku nan Bauchi da Dass hari, an kona gidaje 10 da motoci da dama sakamakon rikicin.
“Gwamnatin Jihar Bauchi, ta shigar da Yakubu Dogara kara tare da wasu mutum 28 a kan lamarin,” inji Galadiman Bauchi.

About andiya

Check Also

Muna Kokarin Kafa Hukumar Da Za Ta Hada Hukumomi Wuri Daya Ne – Honarabul Gumi

Bashir Bello majalisa Abuja Honarabul Suleiman Abubakar Gumi wakilin kananan hukumomin Gumi da Bukkum a …

Leave a Reply

Your email address will not be published.