Daga Imrana Abdullahi
Fitaccen Dan takarar jurerar majalisar dattawa daga mazabar Kaduna ta tsakiya Alhaji Shetima Yerima, ya bayyana rawar da Yan jarida ke takawa wajen Gina kasa a matsayin abin a Yaba ne.
Dan takarar Sanata Shetima Yerima ya bayyana hakan ne a lokacin da Yake tattaunawa da Manema labarai a Kaduna Jim Kadan bayan kammala Taron shekara shekara na makon Yan jarida da aka yi a otal din Bafara cikin garin Kaduna.
“Hakika rawar da Manema labarai wato Yan jarida ke takawa abin a Yaba ne domin sune Ginshikin tabbatar da dorewar taarin dimokuradiyya kuma da mu da ke aikin kungiyoyin kare hakkin al’umma ta hanyar kungiyoyi masu Zaman kansu da Yan jarida hakika muna kokartawa wajen tabbatar da kare tsarin dimokuradiyya, kuma wani Babban al’amarin Shi ne Yan jarida ne suke kokarin taimakawa Jama’a har su Kai wuraren da BA su yi tsammani ba, wannan ni shaida ne a Kan hakan.
“Saboda haka ne ya sa muke kokarin hada Kai tare da Yan jarida a koda yaushe domin samun ingantacviyar Nasara a kasa Baki daya”.
A game da batun yawan Yan takarar kujerar majalisar dattawa daga mazabar Kaduna ta tsakiya kuwa da masu Neman kujerar suka Kai a kalla Goma zuwa Sha daya kuwa sai ya Kada Baki ya ce, “Lallai ni ba na yin Riga Malam Masallaci a Kan kowace irin harka Amma abin da na Sani Shi ne cewa mutane sun waye kwarai sun kuma waye Sosai da irin abubuwan da suka faru a can baya sun kuma waye da dukkan abubuwa da Halayyar da kowa ke nuna wa don haka ni abin da na Sani Shi ne in bayar da kaina domin yi WA Jama’a Hidima don haka dukkan abin da jama’ar suka yanke hukunci mun godewa Allah
Kungiyar Yan jaridu ta kasa reshen Jihar Kaduna sun bayar da lambar karramawa ga Shetima Yerima Sakamakon irin namijin kokarinsa wajen ciyar da rayuwar al’umma gaba.
THESHIELD Garkuwa