A kokarin Gwamnan jihar Katsina Dokta Dikko Umar Radda na ganin an ci gaba da samawa Matasa ayyukan yi yasa ya kirkiro da hukumar samawa Matasa ayyukan yi da koyar da sana’o’in Hannu domin dogaro da Kai.
Hakan ta Sanya Gwamnan ya samu wani jajirtaccen jagoran da ke shugabantar hukumar karkashin jagirancin Honarabul Ya’U Ahmad NOA, Wanda ke ta kokarin zagaya jihar Katsina domin Tara Matasa a kuma Fadakar da su irin yadda Ake cike gurabun Neman ayyukan Soja,Dan Sanda da Sauran ayyukan dammara domin a samu manyan gobe da za a yi alfahari da su.
Gwamna Dikko Umar Radda ya ba wannan hukumar Samar wa mataa aikin yi Wanda Sakamakon hakan an samawa Matasa aikin sarkin guda 2888 a jihar katsina.

Muna yin Kira ga Matasa da su yi amfani da wannan damar da Gwamna Dikko Umar Radda ya runguma domin samawa Matasa aikin yi a duk fadin jihar.
“Neman aikin yi ya tashi daga inda aka San Shi ya na rubuta takardar a aika zuwa yin amfani da ya at gizmo.
“Muna samun matsalar rashin iya yin amfani da na’urar yanar gizo da kuma rashin iya yin aiki musamman yin amfani da ka’idar yin amfani da kwamfuta
Hakika akwai muhimmancin Matasa Su tashi gadan gadan wajen koyon Sana’a
Matasa Su kawar da girman Kai na kin koyon sana’ar hannu

Ma’aikatar gwannati sai Mai matsayin darakta Ake BA naira dubu dari da hamsin Sabanin wadanda suka koyi Sana a sai mutum Mai sana’ar Hannu ya samu makudan Kudi Sama da abin da darakta ke samu
THESHIELD Garkuwa