Home / Labarai / An Yi Gyara A Kan Dokar Zirga Zirgar Babura A Jihar Katsina

An Yi Gyara A Kan Dokar Zirga Zirgar Babura A Jihar Katsina

Dangane da kalubalen tsaro da ake fuskanta a baya-bayan nan a wasu kananan hukumomi a Jihar Katsina, ya sa Gwamnatin Jihar ta yi gyara a kan batun dokar Keke Napep da kuma Baburan hawa inda a yanzu dokar ta koma daga karfe 10 na Dare zuwa karfe 6 na safe.

Kamar dai yadda wata sanarwar da ta fito daga ofishin kwamishinan kula da harkokin tsaro na Jihar ta yi bayanin cewa an dai cimma wannan matsaya ne a zaman taron majalisar tsaro da aka gudanar a ranar 12 ga Satumba, 2023, a gidan gwamnati dake Katsina.

A can baya dai an kafa Dokar hana zirga-zirga a baya wacce ta haramta motsi daga karfe 8:00 na safe zuwa 6:00 na safe.

Kamar yadda sanarwar ta yanzu ta bayyana cewa an yi gyara a kan dokar da aka yi da  za ta fara aiki ne daga 10:00 na safe zuwa 6:00 na safe kullum.

Kwamitin sulhun ya bayyana godiyarsa ga mazauna kananan hukumomin da abin ya shafa bisa hadin kai da goyon bayan da suka ba su wajen bin wannan doka.

Gwamnati da hukumomin tsaro sun amince da muhimmiyar rawar da al’umma ke takawa wajen tabbatar da tsaro.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin mai girma kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida ta tabbatar wa jama’a cewa ana ci gaba da tsare-tsare da kuma kokarin magance matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.

Kuma Gwamnati na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaro da jin dadin ‘yan kasarta.

Sannan Kananan hukumomin da abin ya shafa da dokar hana zirga-zirgar dare ta shafa sun hada da Jibiya, Batsari, Safana, Danmusa, Kankara, Faskari, Sabuwa, Dandume, Danja, Funtua, Kafur, Malumfashi, Musawa, Matazu, Bakori, Dutsinma, Kurfi, Kankiya, da kuma karamar hukumar Charanchi.

Wannan gyare-gyaren yana da nufin samun daidaito ne tsakanin matakan tsaro da jin daɗin mazaunan da suka dogara da waɗannan hanyoyin sufuri a cikin sa’o’in su na dare.

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.