Wani fitaccen dan siyasa da ke karamar hukumar Talatar Mafara a Jihar Zamfara Honarabul Bashir Nafaru, ya yi kira ga Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Dokta Dauda Lawal ta hanzarta daukar matakin da ya dace a kan hanyar Gusau Zuwa Talatar Mafara da ta koma kamar Sambiza.
“Hakika muna yin kira ga Gwamnatin Jihar Zamfara da ta taimaka mana wajen magance matsalar tsaron da ke addabar hanyar Gusau zuwa Talatar Mafara da ta zama kamar Iraki, yankinan da suka kunshi Talatar Mafara, Maradun, Gusau wurin nan akwai matsala saboda mu a ganin mu kamar wani koma baya ne a tsarin kokarin da Gwamnatin take yi wajen ganin an magance matsalar tsaro, hakan kamar koma baya ne”.
Nafaru ya ci gaba da cewa wannan hanya na kawo wa Jihar Zamfara harkokin alkairi kuma suma mutanen Jihar Zamfara na kai wa duniya harkokin alkairi, saboda haka ne muke yin kira ga Gwamnatin da ta Sanya jami’an tsaro a kan hanyar nan su rika yin sintiri domin tsaro ya inganta.