Related Articles
An Yi Taron Tunawa Da Ranar Mata Duniya A Kaduna
Mustapha Imrana Abdullahi
An yi kira ga daukacin matan Jihar Kaduna da Nijeriya baki daya da su mayar da hankali wajen tsayawa domin neman mukamai daban daban ta yadda suma za su samu damar a dama da su kamar yadda ya dace.
Sakatariyar kungiyar Kwadago ta kasa reshen Jihar Kaduna Christiana J. Bawa, ta yi wannan kiran a wajen babban taron ranar mata ta duniya da aka yi a Kaduna.
Sakatariya Christy Bawa ta bayyana wa mata irin muhimmancin da ke akwai na fitowa domin tsayawa neman mukamai daban da ban da nufin tabbatar da gyara a kasa baki daya.
” Hakika mata na da mihimmiyar rawar takawa wajen ciyar da kasa tare da al’ummarta gaba don haka mata su daina tsayawa baya a kowane lokaci su kasance a gaba gaba wanda hakan zai bayar da damar cimma nasarar da ake bukata”.
Taken taron na Bana dai an yi masa lakabi ne da cewa tunkarar kalubalen da za a iya samu na bambance bambance da kalubalen tsaro a wannan lokacin.
Bawa ta ci gaba da cewa su na kira ga mata da kada su rinka jin kunya ko tsoro a wajen fitowa neman zabe ta fuskar siyasa ko kuma neman wadansu mukamai a dukkan matakai baki daya.
Ta kuma kara fadakar da mata cewa a koda yaushe su zama ana daukar matakan cimma matsaya tare da su a wajen tarurruka ko a duk lokacin da suka samu kansu a fagen wata tattaunawa, wanda hakan zai taimakawa daukacin mata su samu biyan bukata.
“Mata ne iyaye masu samar da kasa da kuma bunkasa ta a koda yaushe don haka ku ci gaba da kokarin yi wa yaya tarbiyya a kowane mataki, mata ne masu tabbaci wajen ci gaban al’umma baki daya”.
” Hakika ni ina shaida maku cewa idan da Mahaifin na da rai da kafin in sayi motar hawa da sai na says masa kafin in sayawa kaina domin Mahaifin yakasance mai kokari da son yayansa, shi yake yi mana wanka muna yara ya rika yi mana dukkan abin da ya dace har ya kai mu makaranta kasancewarsa mai son ganin yayansa sun zama mutane a cikin al’umma”, inji Christisns.
Da take gabatar da jawabi shugabar mata a shiyyar Arewa maso Yamma a kungiyar masu gabatar da shirye shirye da wasan kwaikwayo ta kasa Jamila Ahmad Mai damma, cewa ta yi hakika ya dace a jinjinawa kungiyar Kwadago ta kasa reshen Jihar Kaduna kasancewarsu sun yi kira ga mata a kokarin ganin ana damawa da su a dukkan fannin ci gaban rayuwa.
Ta ce mace fa uwa ce a koda yaushe, ba kuma muna cewa mun fi maza ba ne don haka muna fatan alkairi a koda yaushe.
Da take tofa albarkacin bakinta shugabar kungiyar mata yan jarida ta kasa reshen Jihar kaduna Hajiya Fatima Aliyu, kira ta yi ga mata su Jajirce a koda yaushe domin samun ciyar da kasa tare da al’ummarta gaba.
Hajiya Fatima ta kuma yi kira ga Gwamnati da ta kara himma wajen samar da tsaro a dukkan kasa baki daya kasancewar ana wani yanayi ne na satar jama’a a wurare daban daban.
Suma da suke tofa albarkacin bakinsu Misis Polyna Tanze Haruna da Shugabar mata a kungiyar kwadago ta kasa reshen Jihar Kaduna Misis Matha bayani suka yi a kan halin da ake ciki a cikin gidaje na rayuwar yau da kullum inda suka ce yanayin na matukar bukatar daukar matakan gaggawa domin samun kwalliya ta biya kudin sabulu.