Home / News / Muna Tare Da Gwamna Zulum Dari Bisa Dari – Yan Majalisa

Muna Tare Da Gwamna Zulum Dari Bisa Dari – Yan Majalisa

Muna Tare Da Gwamna Zulum Dari Bisa Dari – Yan Majalisa
Mustapha Imrana Abdullahi
Yan majalisar dokokin Jihar Borno karkashin jagorancin shugaban majalisar Abdulkarim Lawan sun bayyana cewa su su na nan tare da Gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum dari bisa dari don haka batun da wasu ke yadawa a kafafen yanar Gizo babu kamshin gaskiya.
Majalisar dai ta yanke wannan hukuncin ne a lokacin da majalisar ta yi wani zaman musamman domin tabbatar wa da duniya batun da wasu ke yadawa a wasu kafafen yanar Gizo da cewa babu kamshin gaskiya a cikin labarin ko kadan.
Yan majalisar sun ce ” hakika su na tare da Gwamna Zulum dari bisa dari domin tare suke tafiyar da ayyukan ciyar da Jihar gaba, dare, rana, ruwa da Iska su na nan tare da Gwamna Zulum wajen tafiyar da Jihar Borno domin samun ci gaban da kowa ke bukata”, inji Majalisar.
Hakazalika majalisar ta kuma yi kira ga hukumar tsaron yan sandan farin kaya masu gudanar da aiki cikin sirri da su gaggauta bincikowa tare da kamawa a kuma gabatar da duk wanda aka samu da hannu wajen kitsa wannan labarin mara tushe balantana makama domin abin da aka yada karya ne kawai.
Wasu daga cikin yan majalisar sun bayyana lamarin da cewa ya yi kama da abin da wasu yan siyasa da ke kokarin cimma birinsu me neman yin amfani da wannan hanya domin cimma buri kawai.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.