Home / Labarai / An Yi Tir Da Kalaman Gwamna Samuel Ortom

An Yi Tir Da Kalaman Gwamna Samuel Ortom

An Yi Tir Da Kalaman Gwamna Samuel Ortom
…..Gwamna Samuel Ortom Na Banuwai Na Kan Garwashin Wuta
Mustapha Imrana Abdullahi
Kungiyar matasan Nijeriya da ke kokarin fadakarwa tare da wayar da kan al’umma ta Nijeriya ta yi Tir da Allah wadai da irin kalaman Gwamnan Jihar Banuwai da ya Jefa a kan Gwamnan Jihar Bauchi.
Kungiyar matasan Nijeriya da ke fadakarwa tare da wayar wa al’umma da kawunansu ta kasa (NIYEM) ta bayyana wa manema labarai a Kaduna cewa kalaman Gwamnan Banuwai da ya jefi Gwamnan Bauchi Bauchi su na ce masa wai “dan ta’adda” hakika irin wannan malamai ba su da amfani ko kadan.
A lokacin taron manema labarai a Kaduna kwamared Sammani Sherif Bashir da Malam Yusuf Abubakar duk sun shaidawa manema labaran cewa kalaman Gwamna Samuel Ortom ba su da amfani ko kadan “ya dubi Gwamna mai shugabantar mutane. Jihar Bauchi kuma tsohon Sanata, tsohon ministan Abuja a tarayyar Nijeriya, ta yaya wani zai yi masa irin wannan kalamai marasa amfani”.
Ya kamata dukkan sauran shugabanni su yi ko yi da irin yadda Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhamamd ya yi kasancewa mutum na farko da ya kaiwa wadanda aka yi wa Ta’adda ta hanyar kai masu hari a garin Sasha Ibadan a Jihar Oyo dauki domin su samu saukin rayuwa.
“Kai had yanzu akwai wadansu mutane a garin da aka kaiwa yan Arewa hari suna fama da rayuwa don haka suna neman dauki sakamakon irin yadda aka lalata masu dukiya”.
A maganarsa lokacin taron manema labaran a Kaduna Malam Yusuf Abubakar ya jawo hankalin Gwamnati cewa babu inda duk fadin duniya ake samun warware wata matsala da karfin tsiya ko kaiwa wani bangare hari, saboda haka a dawo a san irin yadda ya dace a dai-daita a kuma samo bakin zaren.
Takardar manema labaran ta yi bayanin cewa Gwamnan ya zamo wani hadari a game da batun zaman lafiya, siyasar ci gaban jama’a da hadin kan arewacin Nijeriya.
“Ya na da kyau a matsayin shugaba ya rika sanin irin kalaman da zai yi domin irin wannan subutar baki zai kara Jefa al’umma ne cikin wani halin rashin tabbas.
“Irin harin da aka kaiwa wadansu Hausawa yan kasuwa a kasuwar Sasha, Ibadan da ke Jihar Oyo wanda sanadiyyar harin ya haifar da asarar dimbin dukiyar hausawan da suke kasuwanci a Sasha Ibadan”.
Saboda haka muna kira ga masu hannu da shuni da ke da Kumar Susa da su hanzarta zuwa kaiwa wadanda suka yi asarar nan dauki domin suna can a garin Sasha inda suke kasuwanci suna neman taimako sakamakon irin yadda aka lalata masu dimbin dukiyar da suke da ita.
Sai dai ” muna kokarin jaddada cewa ba zamu bari wani ko wasu su dauki doka a ganinsu ba da sunan ramuwar gayya saboda abin da ya faru a Jihohin Ondo a garin  Akure da kuma Ibadan Oyo”.
“Ba kuma muna cewa a cikin kabilar Fulani ba batagari ba, a kowace kabila a cikin Nijeriya za a iya samun wanda ya kasance batagari”.
“Ya dace Yarbawa su ko yi irin yadda za su zauna tare da Juna da kuma kowace kabila a Nijeriya. Ya kuma dace mu rika mijinta Juna ta hanyar bayar da kariya ga kowa da kowace kabila ba tare da tunanin wani bambanci ba”.
Sun kuma yi kira ga shugaban kasa Muhamamdu Buhari da su kara yawan kudin da ake warewa bangaren tsaro musamman ta fuskar samar da makaman zamani, samara da horaswa ga jami’an tsaro a kasa baki daya..
Malam Yusuf Dingyadi ya kuma kira cewa Gwamnatocin Jihohi su yi ko yi da irin yadda takwaransu na Sakkwato ya yi wajen inganta wuraren da makiyaya suke inda ya sama masu da abubuwan mare rayuwa da ya dace a samu wanda hakan ya taimaka kwarai wajen ci gaban ingantar lamarin tsaron da ake samu a Jihar baki daya.
Yayan kungiyar NIYEM ta kuma bayar da shawara ga ministan tsaro wanda ya kasance tsohon Janaral na soja kuma tsoron Gwamna a mulkin soja fa shi kuma a yanzu ya kasance shi ne ministan tsaro a Nijeriya Bashir Salihi Magashi da ya roki gafarar jama’ar kasa a kan irin kalamansa da ya yi na cewa mutane su fito domin yin amfani da Sanda ko wani makami ga masu kaiwa mutane hari da bindiga, “hakika irin wannan kalamai ya dace a duba su sosai domin a Nijeriya mutane da yawa sun rasa rayuwarsu a lokacin yakin Boko Haram da sauran hare haren da ake kaiwa yan Nijeriya a wurare daban daban”.
“Bai dace wani ko wasu su rika yin wasa da kasancewar Nijeriya a matsayin gaba a duk lokacin da wasu za su yi tunani kafin ma su furta kalamai, don haka muke kira ga Gwamnatin tarayya da ta tashi tsaye wajen kare lafiya da dukiyar jama’a daga masu kaiwa mutane hari ba gaira ba dalili”.
Kungiyar  NIYEM  ta yi kira ga masu son zaman lafiya da ci gaban kasa ba tare da la’akari da wani bambanci ba da kowa ya bayar da gudunmawarsa domin cimma nasarar da ake bukata a kasa baki daya.
Saboda kasancewar Nijeriya kasa daya al’umma daya na gaba da komai kuma na gaba da duk wani mutum kowane ne shi komai muhimmancinsa da yake tunani.

About andiya

Check Also

Gwamna Radda Ya Koka Da Cewa  22 LGAs Marasa lafiya A Katsina

Gwamnan jihar Katsina, Dakta Dikko Umar Radda ya koka kan matsalar tsaro a jihar Katsina, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.