Related Articles
An Yi Wa Shugaba Muhammadu Buhari Rigakafin Korona
Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban tarayyar Nijeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo dukkansu an yi masu allurar rigakafin cutar Korona mai nau’in 1A da B.
Babban mai duba lafiyar shugaban kasa Buhari Dokta Suhayb Rafindadi Sanusi ne ya yi wa shugaban allurar a cikin fadar shugaban kasa ta Nijeriya.