Related Articles
Imrana Abdullahi
Gamayyar yan takarar kujerar shugabancin PDP tare da jama’arsu a Jihar kaduna sun koka game da abin da suka bayyana da cewa wadansu mutane a cikin jam’iyyar na neman yi masu wakaci ka tashi ta hanyar karfakarfar kafa masu shugaba.
Gamayyar yan takarar sun shaidawa manema labarai a Kaduna cewa akwai wadansu da ke neman yin amfani da sunan yankin Kudancin Kaduna su domin su kafa shugabancin son zuciyarsu.
“Ta yaya zaka yi wa mutum Aski bayan aba ganinsa?
Kuma ta yaya ” za a kira taro bayan akwai wadanda suke da alhakin kiran taron yaya jam’iyya amma ba a tuntubi zababbun yayan jam’iyya irinsu dan majalisar Dattawa kamar su Sanata Laah da sauran yan majalisar da suka ci zabe a karkashin jam’iyyar PDP”. Inji Gamayyar yan takarar PDP mutum hudu.
Masu takarar shugabancin PDP na Jihar kaduna da suka kafa wata kungiya mai sunan “PDP Chairmanship Aspirants” sun hada da Chief Abubakar Gaiya Haruna, Honarabul Bulus Kajang, Honarabul Ado Dogo Audu da Honarabul Ashafa Waziri duk sun tsame kansu daga taron da ake kokarin yi kamar yadda suka ce a gobe
“Muna sane da irin yadda wadansu ke kokarin kiran taron jama’a da sunan Kudancin Kaduna domin a kakaba wani a shugabancin PDP a Jihar Kaduna”. Inji yan takarar.
Kamar yadda gamayyar yan takarar PDP suka bayyana cewa tun asali yan takarar shugabancin PDP a Jihar Kaduna su shida (6) ne da duka hada da Honarabul Tanko Rossi da tsohon shugaban PDP na Kaduna Mista Felix Hassan Hyat.
Kuma sun tuna wa tsohon shugaban na PDP da cewa ya tuna ko a zamansa shugaba fa wadansu ne suka janye masa sannan ya zama.