Home / Labarai / Ana samun ci gaba ne kawai ta hanyar zaman lafiya – Sanata Danjuma Laah

Ana samun ci gaba ne kawai ta hanyar zaman lafiya – Sanata Danjuma Laah

Ana samun ci gaba ne kawai ta hanyar zaman lafiya – Sanata Danjuma Laah

Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar yankin kudancin Kaduna Sanata Danjuma Tella Laah ya yi kira ga jama’ar yankin da su ci gaba da wanzar da zaman lafiyar da ta fara samuwa a yankin, ta hanyar rungumar juna tare da yin watsi da banbancin addini da na kabila, inda yace ci gaba kowane iri ne yana samuwa ne kawai ta hanyar zaman lafiya

Sanata Danjuma Laah yayi wannan kiran ne a wajen liyafar cin abinci da musulman ‘Majalisar Gidan Man Falke’ suka shiryawa abokan zamansu kiristoci don taya su murnar wucewar azumi da salla lafiya, inda ya bayyana jin dadinsa da yunqurin farfaxo da alaqar da aka San musulmai da kirista da shi tuntuni kafin al’amura su fara dagulewa.

Yace irin haka na taimakawa sosai wajen kara kulla alakar zumunci da kuma taimakawa wajen bunkasa zaman lafiya tsakani.

Yace a duk lokacin da musulmai da kirista suka rungumi junansu tare da fahimtar kansu, to babu wani da zai zo daga nesa da zai ci nasarar shiga tsakaninsu, inda ya sha alwashin samar da hadin kai da fahimtar juna a tsakanin jama’ar shiyyarsa.

Sannan ya shawarci sauran qungiyoyi da majalisu na jama’a da su yi koyi da irin wannan aikin da Majalisar Falke su kayi don kusanto da juna da kuma karin hadin kai.

Sannan ya shawarce su da su fadada irin wannan yunkurin zuwa ga dukkanin kananan hukumomi takwas da ke kudancin Kaduna, inda yayi alkawarin taimaka musu a kan wannan yunkuri mai matukar fa’ida.

Yayinda suke jawabinsu a lokuta daban-daban a wajen liyafar, tsohon Dan Majalisar Wakilai ta Tarayya da ya wakilci kananan hukumomin Jama’a da Sanga, Ado Dogo Audu, da Dan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai ci, Shehu Garba Sarkin Noma (Wanda Alhaji Abbas Sanga ya wakilta), da shugaban qaramar hukumar Jama’a, Peter Averik (Wanda sakataren karamar hukumar Amos Sama’ila ya wakilta), da Dan Majalisar Dokoki na jihar Kaduna mai wakiltar maramar hukumar Jama’a, Ali Kalat duka sun yabawa majalisar bisa ga kyakkyawan tunanin da su ka yi wajen shirya wannan liyafar duk da cewa an kwana biyu da kammala azumi da bikin karamar sallah amma lokaci bai kure ba wajen shirya irin wannan taro mai matukar tasiri da amfani ba.

Sun ce irin haka ke gudana a shekarun saba’inoni da tamanoni (70s da 80s) lokacin da ake zaman lafiya inda mutane a lokacin me kallon kansu a matsayin ‘yan uwan juna ba tare da wariya ko kyamar addinin juna ba.

Yayin da ya me jawabi tunda farko, shugaban majalisar gidan man falke da ke garin Kafanchan, Alhaji Ali Fadi yace basu makara ba wajen shirya wannan liyafar ganin irin muhimmancin da ke ciki da kuma saqon zaman lafiyar da ya ke dauke da shi.

Ali Fadi ya kara da cewa da zaran an dauke dokar hana zirga-zirga za su fara shirye-shiryen yadda za su fadada tarukan zaman lafiya zuwa ga dukkanim kananan hukumomin kudancin Kaduna da ake da su a shiyya ta uku don tabbatar da an samu zaman lafiya mai dorewa.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.