Kasancewar an gudanar da zaben shugaban kasa da na yan majalisun tarayya da na Dattawa a tarayyar Najeriya tun bayan kawo karshen mulkin soja a shekaru 23 da suka gabata a halin yanzu hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ta aiwatar da zaben sun fara sanar da wasu zabukan, hakan ya sa hukumar ta sanar da sakamakon zaben mazabar dan majalisar Funtuwa da Dandume.
Kamar dai yadda hukumar ta sanar ya nuna cewa APC ta lashe zaɓen mazaɓar Funtua/Dandume
Barista Abubakar Mohammed Ahmad Gardi na jam’iyyar APC ya lashe zaben dan majalisar tarayya ta mazabar Funtua/Dandume.
Barista Mohammad Ahmad ya doke Honorable Abubakar Salisu ASAS na jam’iyyar PDP da sauran ƴan takarar.
Ga dai yadda sakamakon zaben ya kasance a Mazabar Funtua da Dandume
APC – 23,901
PDP – 14947