Home / Labarai / Arewa Na Cikin Garari Da Turaddadin Tsaro- Dingyadi

Arewa Na Cikin Garari Da Turaddadin Tsaro- Dingyadi

Daga Imrana Abdullahi

Kungiyar Dattawa da kuma gurguzun matasan yankin arewacin Najeriya sun shaidawa Gwamnatin tarayyar Najeriya irin matsalar tsaron da yankin ke fama da shi da suka ce hakika sai Gwamnatin ta kara kaimi wajen magance matsalar.

Wani dan Gwagwarmaya kuma mai yin sharhi a kan al’amuran yau da kullum wanda ya jagoranci taron kungiyoyin fafutukar nemo yancin yan arewacin Najeriya tare da yankin baki daya Alhaji Yusuf Dingyadi ne ya bayyana hakan a wajen wani taron manema labarai da ya gudana a Kaduna.

Alhaji Yusuf Dingyadi ya ci gaba da bayanin cewa suna kira da kuma yin roko ga shugaba Bola Ahmad Tinubu da ya yi wa Allah ya waiwayo yankin, ya mayar da hankalinsa dari bisa dari wajen magance matsalar tsaron da ake fuskanta.

Tinubu ya bari har sai yankin Arewa ta samu dama ta yin Noma,kiwo da gayruwar tattalin arzikin yankin don haka ne muke yin kira gare shi da duk wani matakin da zai dauka lallai ya dauka har sai yankin Arewa ya samu gyaran da ake bukata.

Hakazalika Yusuf Dingyadi ya yi kira ga wadanda ke cewa sune Dattawan arewacin Najeriya da suke rike da mukamai ko suka rika mukamai a baya da manyan Sarakuna da shugabannin mu da yan Bokon mu da wadanda ke rike da madafun iko da su waiwayo gida domin halin da yan Uwansu ke ciki a Arewa lallai tura ta kai Bango, domin matsalar talauci da wahalhalun da ake ciki sun kai intaha har an kai yanayin da mutane ke ciki ya zama wani lamari kazami mara misaltuwa da ba dadin ji ko kadan,mutane na cikin wahala da bala’i kala kala saboda haka shugabannin Arewa su hada kansu.

A daina zagin Juna a kafofin yada labarai don kawai ra’ayin siyasa a daina zage zagen cewa wai don ni ina dan jam’iyya Kaza ko ba ina dan jam’iyya Kaza ba, a mayar da hankali kawai wajen ceton Arewa domin sai da mutane ne, yanki, Jiha da al’umma zaka iya neman mukami sannan ka iya rayuwa don haka idan muka bari wadannan bala’o’in suka ci gaba to, za a wayi gari ba wai zabe ba ko an kira mutum ya yi takara ba zai yi ba don haka a dauki matakan ceton yankin arewacin Najeriya kuma Najeriya daya al’umma daya sai dai kowa ya san gidan Ubansa.

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.