Home / Ilimi / Gwamna Dikko Radda Ya Dauki Nauyin Dalibai 41 Masu Karatun Likitanci

Gwamna Dikko Radda Ya Dauki Nauyin Dalibai 41 Masu Karatun Likitanci

 

Daga Imrana Abdullahi
Gwamnatin Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda PhD za ta dauki nauyin karatun dalibai 41 zuwa kasar Masar don karatun likitanci.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Isah Miqdad mai taimakawa Gwamnan Jihar Katsina a kan kafofin yada labarai na zamani da aka rabawa manema labarai.

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD Zai Kaddamar Da Shirin daukar nauyin  karatun dalibai 41 zuwa Kasar Masar da za su yi karatun digiri na farko a likitanci (Medicine) a jami’ar Kasar ta Nahda University, Cairo.

Bikin kaddamar da shirin da kuma ba da takardun shaidar shiga jami’a na ‘admission letter’ zai gudana ne a fadar Gidan Gwamnatin Jihar Katsina a ranar Litinin, 22 ga watan Janairu 2024 da misalin karfe 10:00am na safe.

Wannan yunkurin na daga cikin kudirin Gwamna Malam Dikko Umaru Radda wajen ganin ‘ya’yan talakawa sun samu Ilimi ingantacce da kuma shawo kan karancin likitoci a Jihar Katsina.

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.