Home / News / Asake Ya Kai Wa Sarkin Zazzau Ziyara, Ya Tabbatar Masa Da Hada Kan Jama’a Da Ci Gaban Jiha

Asake Ya Kai Wa Sarkin Zazzau Ziyara, Ya Tabbatar Masa Da Hada Kan Jama’a Da Ci Gaban Jiha

Daga Imrana Abdullahi
Gabanin zaben Gwamnonin da za a yi a ranar 11 ga watan Maris mai zuwa dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar Lebo Honarabul Jonathan Asake ya kai wa mai martaba Sarkin Zazzau wanda shi ne shugaban majalisar Sarakunan Jihar Kaduna Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ziyara a fadarsa.
Asake ya kuma Gabatarwa mai martaba Sarkin kundin manufofin kamfe dinsa inda ya shaidawa Sarkin cewa jam’iyyar Lebo ce keda ainihin kundin mafi yau kuma ya ce ya na da ingantaccen kyakkyawan tsarin samar da hadin kai da ciyar da Jihar Kaduna gaba domin fita daga cikin halin kangin da ake ciki.
Ya ce kudirorin da ya fitar guda biyar an samar da su ne ta hanyar yin bincike kuma daga baya aka hada su wuri guda domin samar da mafita ga Jihar Kaduna ta hanyar kokarin samar da mafita na jam’iyyar Lebo.
“Muna da kyawawan shirye shirye guda biyar da suka kasance ginshikai. Abu na farko dai shi ne batun tsaron lafiya da dukiyar jama’a. Sai na biyu kulawa da harkokin wasanni, Mata da karfafa Matasa.Sai kuma abu na hudu shi ne samar da ingantaccen tattalin arzikin da kowa zai amfana da shi tare da samar da abubuwan more rayuwa. Sai na biyar shi ne samar da bangarorin Gwamnati masu karfi da inganci”, inji shi.
A ciki wata  takardar da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun mai taimakawa dan takarar Gwamnan a kan harkokin yada labarai, James Swam, ya ba Ssrkin tabbaci tare da al’ummar Zariya cewa zai yi jagorancin Jihar Kaduna da nuna gaskiya da adalci.
Ya kara jaddada cewa idan an zabe shi a matsayin Gwamnan Jihar Kaduna,jam’iyyar Lebo za ta tabbatar da cewa “an Kare mutunci da martabar Talakawa daga matsalar tsaro, yunwa da talauci wanda da gangan aka bari ya shiga jama’a duk sakamakon munanan manufofin da suka ragargaza al’umma”.
Asake ya nuna bacin ransa game da kasawar Gwamnati na yin maganin matsalar tsaron da ke addabar kasa, sai ya bayar da tabbacin cewa babban abin da zai mayar da hankali kenan wajen magancewa idan ya samu nasara.
Da yake mayar da jawabi mai martaba Sarkin Zazzau cewa ya yi tsaron lafiya da dukiyar jama’a tare da zaman lafiya ne babban abin da kowa ke bukata, Sai ya bayyana bacon ransa game da matsalar tsaro musamman na satar jama’a a yankin karamar hukumar Giwa.
Sarkin na Zazaau sai ya bayar da shawara a kan samun mutanta Juna a duk tsakanin wasu kungiyoyi,ya ce babban abin shi ne a samu zaman lafiya koda bayan zabe
Dan takarar Gwamnan na jam’iyyar Lebo ya kuma ziyarci shugaban kungiyar Dattawan Arewa ta NEF, Magajin Rafin Zazzau, Farfesa Ango Abdullahi da kuma Madakin Zazzau Munir Jaafar wanda kuma shi ne dan barhin na Zazzau, Ahmad Bashir Aminu da sauran wadansu muhimman mutane da masu ruwa da tsaki da suke a cikin birnin Zariya.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.