Shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa ,Dokta Iyorchia Ayu , zai bar Najeriya zuwa tarayyar Turai gobe (Laraba).
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun Simon Imobo-Tswam
Mataimakin na musamman ga shugaban jam’iyyar a kan kafafen yaɗa labarai.
Ayu zai kasance baya cikin ƙasar nan har zuwa nan da sati biyu .
Bayan tafiyar sa , mataimakin sa na shiyyar arewa Ambasada Iiya Damagun , zai jagoranci komai .
Shugaban jam’iyyar ya sanar da hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta ya miƙa komai ga mataimaƙin sa .
Zai dawo zuwa ƙarshen wata .