Home / Labarai / AYU ZAI YI TAFIYA ZUWA TURAI GOBE , YA MIƘA RAGAMAR KOMAI GA MATAIMAKIN SA

AYU ZAI YI TAFIYA ZUWA TURAI GOBE , YA MIƘA RAGAMAR KOMAI GA MATAIMAKIN SA

 

Shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa ,Dokta Iyorchia Ayu , zai bar Najeriya zuwa tarayyar Turai gobe (Laraba).

 

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun Simon Imobo-Tswam
Mataimakin na musamman ga shugaban jam’iyyar a kan kafafen yaɗa labarai.

Ayu zai kasance baya cikin ƙasar nan har zuwa nan da sati biyu .

Bayan tafiyar sa , mataimakin sa na shiyyar arewa Ambasada Iiya Damagun , zai jagoranci komai .

Shugaban jam’iyyar ya sanar da hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta ya miƙa komai ga mataimaƙin sa .

Zai dawo zuwa ƙarshen wata .

 

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.