Home / Big News / Ba A Cimma Matsaya A Batun Inda Dan takara Zai Fito Ba – APC

Ba A Cimma Matsaya A Batun Inda Dan takara Zai Fito Ba – APC

 

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
KWAMITIN riko na kasa da aka Dorawa Alhakin gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar APC na kasa ya yi watsi da batun da wasu ke yadawa cewa an mika batun takara ga wata shiyya a zaben da za a yi a ranar 26 ga watan Fabrairu 2022.

Kwamitin ya fayyace karara cewa bayan taron tattaunawar da aka yi karo na 19 da aka kwashe tsawon kwanaki  biyu ana yi, an dai fitar da jadawalin ranakun da za a gudanar da zabe har zuwa ranar  babban taron Jam’iyyar na kasa baki daya.

Da yake yi wa manema labarai jawabi a ranar Laraba a babban ofishin jam’iyyar na kasa, sakataren riko na  babban kwamitin shirya taron na kasa, Sanata John James Akpanudoedehe, ya ce babu wani lokacin da aka tattauna batun cewa wata shiyya kaza ko kaza ne shugaban jam’iyyar zai fito ba.

Akpanudoedehe: “ Na zo nan ne domin in Karyata wani labarin karya da ake yadawa a dandalin Sada zumunta na zamani cewa wai mun yanke shawara a game da batun shiyya shiyyar da shugabannin APC za su fito. A gaskiyar magana har yanzu ba mu zauna don tattauna wannan batun ba.
“Labarin da kuma jita jitar da  yake yawo duk bayanan kanzon kurege ne. Domin sam ba a tattauna wannan batun ba a duk tattaunawar da muka yi. Saboda haka muna kira ga jama’a da kada su amince da wannan batun, saboda duk labarin karya ne. Kuma ba gaskiya ba ne”

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.